Trends

2027: Atiku Abubakar ya Lashe Zaɓen Fidda Gwani na Jam’iyyar ADC

Da yake bayyana sakamakon zaɓen a sakatariyar jam’iyyar da ke Sokoto, jami’in tattara sakamakon zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa a jihar, Farfesa Aminu Abubakar, ya ce an kaɗa ƙuri’u 69,434 daga cikin masu rajista 69,871.

A cewarsa, Atiku ya samu ƙuri’u 68,823 inda ya kayar da sauran masu neman takarar a zaɓen.

Alhaji Muhammad Hayatudeen ya samu ƙuri’u 319, yayin da tsohon gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, ya samu ƙuri’u 292.

An gudanar da zaɓen ne a gaban masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, ciki har da tsohon gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, da tsohon mataimakin gwamnan jihar, Manir Muhammad Dan’iya, da kuma shugaban jam’iyyar a jihar, Abdullahi Maigwandu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *