Trends

Zargin Badakalar: EFCC Ta Kama Shugaban Hukumar Makamashi Kan Biliyan 500

Shugaban Hukumar Yaki da cin Hanci da rashawa ta Kasa Ola Olukoyede

Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) ta kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Najeriya (ECN), Mustapha Abdullahi, bisa zargin safarar kudade da badakalar da ta haura naira biliyan 500.

Rahotanni sun bayyana cewa an kama Abdullahi ne a Abuja ranar Laraba, kuma yanzu haka yana hannun EFCC domin ci gaba da bincike.

Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, bai samu damar yin bayani kan lamarin ba a lokacin hada wannan rahoto.

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ne ya nada Abdullahi a matsayin shugaban ECN a watan Oktoban 2023 bayan ya shafe sama da shekaru goma yana aiki a Hukumar Kula da Harkokin Mai ta Sama ta Najeriya (NUPRC).

A watan Disambar 2025, wata kungiyar farar hula mai suna Network Against Corruption and Drug Trafficking (NACAT) ta aika koke ga Shugaba Tinubu, EFCC da ICPC tana zargin akwai almundahana a hukumar makamashin.

Kungiyar ta zargi Mustapha Abdullahi da jagorantar wata “tsararren badakala” ta bayar da kwangilolin hasken titunan hasken rana da suka kai daruruwan miliyoyin naira ga kamfanoni biyar da ake zargin mutum daya ko rukuni daya ne suka mallake su.

NACAT ta ce an yi rajistar kamfanonin ne cikin mako guda tsakanin karshen Oktoba da farkon Nuwamban 2023, kuma suna da adireshi iri daya a Abuja tare da shugabanni masu kama da juna, wanda kungiyar ta ce ya saba wa dokokin saye da bayar da kwangila na Najeriya.

Kungiyar ta bayyana lamarin a matsayin cin amanar jama’a tare da bukatar hukumomi su gudanar da cikakken bincike tare da hukunta duk wadanda aka samu da hannu.

Kamen na daga cikin manyan shari’un yaki da cin hanci da rashawa a gwamnatin Tinubu, yayin da EFCC ke kara sa ido kan jami’an gwamnati da ake zargi da karkatar da kudaden ayyukan kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *