Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman hukuncin daurin shekaru 75 a gidan yari bisa laifin damfara da safarar kudade har naira biliyan 33.8.
Alkalin kotun, Mai Shari’a James Omotosho, ya same shi da laifi a kan dukkan tuhume-tuhume 12 da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta gabatar a kansa.
Kotun ta ce an tabbatar cewa Mamman ya karkatar da kudaden gwamnati tare da wanke su ta hanyar harkokin banki da aka boye yayin da yake rike da mukamin minista.
A hukuncin da aka yanke, an yanke masa shekaru bakwai a kowanne daga cikin tuhume-tuhume 10, sannan aka kara masa shekaru uku da biyu a wasu tuhume-tuhume biyu daban.
Alkalin kotun ya kuma bayyana cewa hukuncin zai gudana ne a jere (consecutive), wanda ya kai jimillar shekaru 75 a gidan yari, kuma babu damar biyan tara a mafi yawan tuhume-tuhumen da aka same shi da su.
Sai dai kotun ta ba shi damar biyan tara naira miliyan 10 a daya daga cikin tuhume-tuhumen.
Haka kuma kotun ta umarci kwace wasu kadarori da suka hada da kudaden waje da aka gano a lokacin bincike da kuma gidaje hudu masu daraja a Abuja da aka danganta da shi.
Saleh Mamman ya taba rike mukami ne a gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, kuma an gurfanar da shi ne bayan zargin karkatar da kudaden da aka ware domin ayyukan wutar lantarki ta hanyar hada-hadar banki da asusun wakilai.
