Ministan Wutar Lantarki na Najeriya, Joseph Olusunkanmi Tegbe, ya bayyana wasu muhimman abubuwa guda biyar da gwamnatin tarayya za ta mayar da hankali a kai domin tabbatar da daidaitaccen samar da wutar lantarki da kuma farfado da bangaren makamashi a kasar.
A cewarsa, an tsara wadannan manufofi ne domin magance matsalolin da suka dade suna addabar bangaren samar da wuta, watsawa, rabawa, sanya mita, da kuma dorewar harkokin kudin bangaren lantarki.
Ministan ya bayyana cewa abu na farko shi ne inganta samar da iskar gas domin kara karfin samar da wutar lantarki a fadin kasar, yana mai cewa samun wadataccen gas na da matukar muhimmanci wajen kara yawan wutar da ake samarwa.
Ya kuma jaddada bukatar inganta kayayyakin aikin layin wutar lantarki domin kara inganci da rage yawaitar katsewar wuta da ke ci gaba da shafar gidaje da harkokin kasuwanci a fadin Najeriya.
Dangane da bangaren rabon wuta, Joseph Olusunkanmi Tegbe ya ce gwamnati za ta kafa tsauraran matakan sa ido da daukar alhaki ga kamfanonin rarraba wuta domin inganta ayyukansu da kuma samar da kyakkyawan sabis ga al’umma.
Ministan ya kuma bayyana cewa gwamnati za ta gaggauta samar da mitocin wutar lantarki ga kwastomomi domin rage matsalar kiyasin kudin wuta da kuma tabbatar da gaskiya wajen lissafin amfani da wutar lantarki da biyan kudade.
Ya kara da cewa dawo da daidaiton harkokin kudin bangaren lantarki na daga cikin manyan abubuwan da gwamnati ta sa a gaba, yana mai cewa hakan ne zai jawo karin masu zuba jari tare da tabbatar da dorewar bangaren na dogon lokaci.
Joseph Olusunkanmi Tegbe ya sake tabbatar da kudirin Gwamnatin tarayya na ci gaba da aiwatar da gyare-gyare masu muhimmanci domin samar wa ‘yan Najeriya ingantacciyar kuma amintacciyar wutar lantarki.






