An Kama Mata Uku Bisa Zargin Kisan Jami’in Kwastam a Dakin Otel

An kama wasu mata uku da ake zargi da hannu a mutuwar wani jami’in Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS), mai mukamin Assistant Superintendent of Customs, Lawal Tukur, wanda aka samu gawarsa a dakin otel cikin yanayi mai cike da rudani.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da daddare a ranar Laraba, a sanannen otel ɗin Murjani Hotel dake cikin birnin Katsina, inda jami’in ya shiga da misalin karfe daya na rana, amma daga baya aka same shi ba shi da rai.

Abin da ya fara a matsayin kwanciyar hankali da hutun dare, ya rikide zuwa tashin hankali bayan ma’aikatan otel ɗin suka gano gawar Tukur a dakinsa.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa matan da aka kama sune: Khadija Ali (34) daga unguwar Dutsin Amare, Aisha Lawal (30) daga karamar hukumar Ingawa, da kuma Hafsat Yusuf (22) daga unguwar Brigade a jihar Kano. Rahotanni na nuna cewa Khadija da Aisha sun kwana tare da jami’in a dakin otel ɗin, yayin da Hafsat ta iso daga baya kuma ita ma ta kama wani daki a otel ɗin.

Da zarar an gano gawar, shugabancin otel ɗin ya sanar da hukumomi, inda aka garzaya da Tukur zuwa Asibitin Koyarwa na Tarayya Katsina, inda likitoci suka tabbatar da cewa ya riga ya mutu kafin isowarsa.

Yayin da ake ta tambayoyi da cece-kuce, rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina ta kaddamar da cikakken bincike kan lamarin. Majiyoyi daga cikin rundunar sun tabbatar da cewa an kama matan uku din tare da mai otel ɗin, wasu muhimman ma’aikata da wadanda suka yi aiki a daren da lamarin ya faru, domin taimakawa wajen bincike.

Wani babban jami’in tsaro da ya san da al’amarin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa akwai jita-jita da dama da ba su da tushe.

“Eh, lamarin gaskiya ne, amma ba duk abin da ake yadawa gaskiya ba ne. Bincike yana tafiya, kuma muna jiran sakamakon binciken likitoci da na forensik domin gano ainihin musabbabin mutuwar,” in ji jami’in.

Gawar jami’in an ajiye ta a dakin ajiyar gawa na asibitin domin yin autopsy, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da bincike domin gano hakikanin abin da ya faru kafin rasuwarsa.