Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ba ta kammala tsarin bada afuwa ga Maryam Sanda da wasu mutane 81 ba, duk da sanarwar da aka yi a baya cewa an basu afuwa da yafe wa.
Tun a makon da ya gabata ne Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da bayar da afuwar shugaban kasa da sassaucin hukunci ga mutane 175, bayan Majalisar Kasa ta Taro (National Council of State) ta amince da shawarwarin Kwamitin Ba da Afuwa na Shugaban Kasa (PACPM).
A cewar sanarwar da mai magana da yawun fadar shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya fitar, kwamitin ya duba shari’o’i 294, inda aka ba da shawarar a yi wa 82 afuwa, a yafe wa 2, a rage wa 65 hukunci, a sauya hukuncin kisa 7 zuwa zaman gidan yari har abada, tare da ba wa tsoffin fursunoni 15 afuwa bayan mutuwa, ciki har da Ogoni Nine.
Sai dai a cikin wata sanarwa da Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya, Lateef Fagbemi (SAN) ya fitar jiya, ya jaddada cewa har yanzu aikin bai kai ƙarshe ba.
Wasu lauyoyi kuma sun zargi gwamnatin tarayya da kokarin ruɗar ‘yan Najeriya da wannan sanarwar.
An samu martani mai ƙarfi daga jama’a game da jerin sunayen wadanda suka amfana da afuwar, inda mutane da dama suka tambayi dalilin yanke wannan hukunci.
Fagbemi ya bayyana cewa babu ɗan fursuna ko guda ɗaya da aka saki daga kurkuku karkashin wannan tsarin afuwa da aka sanar da shi kwanan nan.
Ya ce:
“Tsarin yana a matakin karshe na gudanarwa, wanda ya haɗa da bincike na ƙarshe don tabbatar da cewa duk sunaye da shawarwari sun cika ƙa’idoji na doka da tsarin gudanarwa kafin a fitar da takardar sakin hukuma.”
Ya ƙara da cewa:
“Mataki na ƙarshe bayan amincewar Majalisar Kasa shi ne fitar da takardar hukuma don aiwatar da shawarar game da kowane mutum. Wannan mataki yana ba da damar sake duba jerin sunaye kafin takardar ta tafi ofishin Shugaban Hukumar Gyaran Hali (Controller-General of Corrections) don daukar mataki.”
Ministan ya bayyana cewa wannan tsarin tantancewa yana nuna gaskiya, bin doka da kulawa da gwamnati ke nunawa wajen gudanar da aiki.
Ya gode wa jama’a bisa kulawa da tsokaci da suke bayarwa, yana mai cewa hakan yana ƙarfafa aminci da ingancin hukumomi.
“Ba a jinkirta aikin ba, ana kawai bin doka ne yadda ya dace don tabbatar da cewa wadanda suka cancanta kawai za su amfana da afuwar shugaban kasa. Da zarar an kammala duba doka da tsarin gudanarwa, za a sanar da jama’a. Doka ba ta gudu; tana tabbatar da adalci,” in ji Fagbemi.
Wadanda Suka Amfana da Afuwar
Cikin mutane 82 da aka ba afuwa akwai Maryam Sanda, mai shekaru 37, wadda aka yanke wa hukuncin kisa a 2020 bayan ta kashe mijinta, kuma ta shafe shekaru 6 da watanni 8 a gidan gyaran hali na Suleja.
Sauran sun haɗa da:
Aluagwu Lawrence (47) – yanke masa hukunci kan sayar da tabar wiwi a 2015
Ben Friday (60) – shekara 3 ko tara N1.3m saboda wiwi (2023)
Oroke Michael Chibueze (21) – shekara 5 saboda tabar cannabis (2023)
Kelvin Christopher Smith (42) – shekara 4 saboda shigo da koka’in (2023)
Azubuike Jeremiah Emeka (31) – shekara 5 ko tara N3m saboda koka’in (2021)
Haka kuma akwai:
Akinrinnade Akinwande (47) – shekara 3 saboda Tramadol (2023)
Ahmed Adeyemo (38) – shekara 15 saboda tabar wiwi
Adeniyi Jimoh (31) – shekara 15 saboda kwayoyi (2015), ya shafe 9 a Kirikiri
Seun Omirinde (39) – shekara 15 saboda kwayoyi (2015), ya shafe 9 a Kirikiri
Adesanya Olufemi Paul (61) – shekara 14 saboda sata, ya shafe 8
Ife Yusuf (37) – saboda safarar mutane (2019), ya shafe 6 a Kirikiri
Sauran sun haɗa da Daniel Bodunwa (43), Fidelis Michael (40), Suru Akande (52), Safiyanu Umar (56), Dahiru Abdullahi (46), Hamza Abubakar (37), Rabiu Alhassan Dawaki (52), Mujibu Muhammad (30), da Emmanuel Eze (49).
Wadanda aka ba pardon (gaskatacciyar afuwa) sun haɗa da:
Farouk M. Lawan (62) – hukuncin shekara 5 saboda cin hanci (2021)
Nweke Francis Chibueze (44) – zaman rai da rai saboda laifin kwayoyi
Dr. Nwogu Peters (67) – hukuncin shekara 17 saboda zamba.
Wadanda aka ba afuwar bayan mutuwa sun haɗa da:
Sir Herbert Macaulay – wanda Turawan mulkin mallaka suka yankewa hukunci a 1913,
Janar Mamman Jiya Vatsa (46) – wanda aka kashe a 1986 saboda zargin juyin mulki,
Ogoni Nine – wadanda aka kashe a 1995.
Lauyoyi Sun Soki Tsarin Afuwar
Wasu lauyoyi da suka yi magana da jaridar Daily Trust sun bayyana cewa wannan sanarwar ta gwamnatin tarayya tana da ruɗani kuma kamar wani yunƙurin ruɗar jama’a ce.
Barrister Gabriel Egbule ya ce wannan shi ne karo na farko da aka taba ganin an fitar da jerin wadanda aka ba afuwa sannan a ce za a sake duba tsarin.
“Abin takaici ne. A kasashen da suka ci gaba, da wani ya rasa aikinsa saboda irin wannan. Wannan abin kunya ne,” in ji shi.
Shi kuwa Barrister Jibrin Jibrin, ya ce abin mamaki ne saboda kafin shugaban kasa ya amince, kwamitin da Majalisar Kasa ya kamata sun tabbatar da duk bayanai.
“Gwamnati ta sanar da sunayen wadanda aka ba afuwa a fili, yanzu kuma suna cewa ba a kammala ba. Wannan abin dariya ne kuma ba gaskiya ba ne,” in ji Jibrin.
Ya kuma tambayi dacewar ba wa wasu da suka tabo lafiyar al’umma irin wannan afuwa.
Barrister EMD Umukoro kuma ya ce tsarin ya kamata ya ƙare bayan an yi shawara da kwamitin ba da afuwa da majalisar kasa, sannan a fitar da takarda (gazette) don aiwatarwa.
“Da zarar hakan an yi shi, al’amarin ya ƙare. Gwamnatoci da suka gabata – kamar Shehu Shagari, Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan – duk sun yi haka,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa wannan matakin na yanzu ya nuna cewa gwamnati ta canza ra’ayi bayan cewa jama’a sun yi ƙorafi sosai kan jerin sunayen.
“A gefe guda, yana da kyau suna sauraron muradun jama’a, amma a gefe guda, ya nuna cewa tsarin bai gudana cikin gaskiya da natsuwa ba,” in ji shi.
Sai dai babban lauya Dayo Akinlaja (SAN) ya bayyana cewa babu wanda ya kamata ya yi ƙorafi, domin yanke irin wannan hukunci na cikin ikon gwamnati ne.
Labari Daga Daily Trust



