Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya ba da umarni ga dukkan mambobin majalisar zartarwar jiharsa da su rika sanya hular “Asiwaju” — hular da ake dangantawa da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu — yayin tarukan majalisar zartarwa (EXCO).
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi ga sabbin kwamishinoni a Birnin Benin a ranar Talata, inda ya ce hular, wacce ke ɗauke da tambarin ɓaɓɓaken sarƙa (broken shackle) da ke zama alamar Tinubu, tana nuna aminci da haɗin kai a cikin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
“Ba zan ji daɗi da kwamishina wanda bai sanya hular Asiwaju ta Tinubu ba. Idan ka halarci taron majalisar ba tare da ita ba, dole ne ka koma ka ɗauko ta,” in ji Okpebholo cikin gargadi.
Gwamnan, wanda ya hau mulki a Nuwamba 2024, ya bayyana cewa wannan tsarin tufafi an ƙirƙire shi ne domin ƙarfafa dangantaka da haɗin kai tsakanin jami’an jiha da na tarayya a ƙarƙashin gwamnatin jam’iyyar APC.
Yayin da wasu magoya baya suka yaba da matakin a matsayin alamar ɗa’a da haɗin kan jam’iyya, wasu kuma sun soki umarnin a matsayin abin ban dariya da nuna son kai na siyasa.
Bidiyon jawabin gwamnan ya bazu a kafafen sada zumunta, inda ya haifar da muƙabala tsakanin mazauna Edo da masu sharhin siyasa, yayin da wasu ke ganin wannan matakin ba shi da mahimmanci a harkar gudanar da gwamnati.



