Gwamnatin Tarayya ta bayyana jin daɗinta bisa hukuncin da kotun Päijät-Häme da ke kasar Finland ta yanke a ranar Litinin, inda ta daure Simon Ekpa, wanda ya bayyana kansa a matsayin mai rajin kafa Biafra, shekaru shida a gidan yari bisa laifin ta’addanci.
A cikin wata sanarwa da Ministan Yaɗa Labarai da Tsarin Ƙasa, Mohammed Idris, ya fitar a ranar Litinin, ya ce wannan hukunci babbar alama ce ba kawai ga dubban ’yan Najeriya marasa laifi da suka fuskanci mummunan tashin hankali da rayuwarsu da harkokinsu na kasuwanci suka lalace sakamakon ayyukan ta’addanci da Ekpa da abokan aikinsa suka shirya ba, har ma ga ƙarfafa dangantakar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Finland.
“Tsawon shekaru, sakonnin tayar da hankali da tsokanar tashin hankali da Ekpa ya rika yi ta hannun ayyukan ta’addancin IPOB sun haddasa bala’i mara misaltuwa: iyalai sun tarwatse, kasuwanci ya rushe, yara sun zama marayu, al’ummomi gaba ɗaya kuma sun kasance cikin tsoro.
An rasa rayuka da dama, wasu kuma suka samu raunuka, saboda wani shiri na rushe ƙasa wanda ba bisa ƙa’ida ba, kuma ya yi barazana ga zaman lafiya, haɗin kai da mutuncin ƙasarmu.”
“Da wannan hukunci, kotun Finland ba kawai ta tabbatar da matsayin Najeriya kan wannan lamari ba, har ma ta aika da sako kai tsaye ga ’yan ta’adda a ko’ina cikin duniya cewa ana kallonsu, kuma shari’a za ta kama su duk inda suka shiga don tada hankali da ta’addanci.”
Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, a cewar ministan, za ta ci gaba da kasancewa tsayin daka wajen kare ikon Najeriya da kuma mutuncin ’yan ƙasa. “Za mu ci gaba da amfani da duk wata hanya diflomasiyya, soji, da shari’a – don kiyaye zaman lafiya, haɗin kai da iyakokin ƙasarmu.”
Ya kuma yi kira ga duk wanda ya biyo bayan Simon Ekpa da sauran masu tayar da hankali da su ajiye makamai, su rungumi hanyar zaman lafiya. “Najeriya ta isa wa kowa, amma ba za a samu ci gaba ba a inda tashin hankali da rabuwar kai ke ci gaba da wanzuwa,” in ji shi.
Gwamnatin Tarayya ta kuma mika godiyarta ga Ofishin Mai Ba da Shawara kan Harkokin Tsaro na Ƙasa, Rundunar Sojojin Najeriya, hukumomin tsaro da leken asiri, Ma’aikatar Shari’a da kuma ’Yan Sanda na Najeriya bisa sadaukarwa da jajircewar da suke nunawa wajen kare ƙasar nan duk da ƙalubale masu tsanani.
“Yayin da muke kallon wannan lokaci a matsayin sabon babi, gwamnatin tarayya na kira ga duk ’yan Najeriya, a ciki da wajen ƙasa, da su haɗa kai don tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da tsaron ƙasar.”

