Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da amfani da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) wajen tsoratar da ‘yan adawa domin tilasta musu shiga jam’iyyar mai mulki.
Atiku ya ce hakan ne ya sa EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, saboda kasancewarsa ɗan ƙungiyar adawa.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafukan sada zumunta a ranar Talata, Atiku ya bayyana cewa tsare Tambuwal da wasu manyan ‘yan adawa “yana daga cikin shirye-shiryen gwamnatin Tinubu na ci gaba da danniya, tsoratarwa, da raunana ‘yan adawa.”
Ya ce abin da ke faruwa yanzu shi ne gwamnatin Tinubu ta maida yaƙi da cin hanci da rashawa kayan aiki na siyasa domin tilasta shugabannin ‘yan adawa shiga jam’iyyar mai mulki.
“Muna gani a fili yadda gwamnati da jami’anta ke kama matsayin mai tsangwama, suna amfani da yaƙi da cin hanci a matsayin ajandar siyasa. Wannan ba shi bane dalilin da ya sa na yi aiki tukuru a lokacin gwamnatinmu wajen kafa EFCC.
Yanzu, duk wanda ya nuna alaka da ‘yan adawa ana ƙirƙiro masa zargin rashawa, amma idan aka tilasta masa shiga shirin siyasar Tinubu, sai a ce an yafewa ‘laifinsa’,” in ji Atiku.
Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen da ya gabata ya ce hanyar da gwamnatin yanzu ke bi ba ita ce hanyar gina ƙungiyoyi masu ƙarfi ba.
“Wannan ba ita ce hanyar yaƙi da cin hanci ba. A gaskiya irin wannan hali yana ƙara ƙarfafa rashawa. Mun shaida yadda ake amfani da EFCC wajen tursasa gwamnonin ‘yan adawa su koma jam’iyyar mai mulki, kuma wannan abin bai kusa ƙarewa ba,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, ko da yake yaƙi da cin hanci na buƙatar haɗin kan ‘yan Najeriya gaba ɗaya, amfani da shi a matsayin ajandar siyasa ya kamata a yi Allah-wadai da shi daga dukkanin masu fafutukar kare dimokuraɗiyya da abokan Najeriya a ƙasashen waje.
A matsayinsa na ɗaya daga cikin shugabannin sabuwar ƙungiyar haɗin gwiwa ta ‘yan adawa, Atiku ya ce:
“Nigeriyawa sun shaida yadda ake amfani da hukumomin yaƙi da cin hanci wajen tilasta shugabannin siyasa shiga jam’iyyar mai mulki. Tabbacinmu ga ‘yan Najeriya shi ne ba za mu taɓa mika wuya ga wannan tsarin danniya da ke ƙoƙarin maida ƙasar nan ƙarƙashin jam’iyya ɗaya ba.”

