Fursunoni 16 sun tsere daga Cibiyar Kula da Fursunoni ta Tsaron Matsakaici (Medium Security Custodial Centre) da ke Keffi, Jihar Nasarawa, da sanyin safiyar Talata bayan da suka mamaye jami’an tsaro tare da karya tsarin tsaro na wurin.
A cewar mai magana da yawun Hukumar Kula da Fursunoni ta Najeriya, Umar Abubakar, jami’ai biyar sun ji rauni a yayin arangamar. Daga cikinsu, biyu na cikin mawuyacin hali kuma ana ba su gaggawar kulawa a asibitin gwamnati. An sake cafke fursunoni bakwai daga cikin waɗanda suka tsere, yayin da bincike da farautar sauran tara ke ci gaba.
A cikin sanarwar Abubakar, ya tabbatar da cewa:
“Wasu fursunoni sun karya tsarin tsaron cibiyar, suka kai hari ga jami’an da ke bakin aiki domin su samu damar tserewa, wanda hakan ya ba fursunoni 16 damar kubuta.”
Bayan faruwar lamarin, Kwamandan Janar na Hukumar Kula da Fursunoni, Sylvester Nwakuche, ya ziyarci cibiyar. Ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan tserewar, tare da gargadin cewa:
“Ba za a bar wani ma’aikaci ba idan aka same shi da laifi.”
Haka kuma ya umarci a gudanar da gaggawar farautar waɗanda suka tsere tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro.
Hukumar ta shawarci jama’a da su kasance cikin natsuwa da faɗakarwa, tare da gaggauta sanar da hukumomin tsaro mafi kusa idan sun ga wani motsi ko mutum da ake zargi daga cikin waɗanda suka tsere.

