PDP ta Zargi Gwamnan Gombe da Bai wa Rarara Kyautar Naira Miliyan 315 da Filaye

Inuwa Yahaya Gwamnan Jihar Gombe

Reshen Peoples Democratic Party (PDP) na Jihar Gombe ya soki gwamnatin jihar bisa zargin bai wa fitaccen mawakin Kano, Dauda Adamu Kahutu (Rarara), kyaututtuka da darajarsu ta kai Naira miliyan 315 tare da ba shi filaye.

A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na jam’iyyar, Abdulkadir Ahmad Dukku, ya fitar, PDP ta bayyana cewa tana matukar damuwa kan abin da ta kira kashe kudaden jama’a da kuma rabon kadarorin gwamnati da gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ta yi.

Jam’iyyar ta yi zargin cewa bayanan da take da su sun nuna gwamnatin jihar ta amince da kashe Naira miliyan 115 wajen sayen motar Coaster ga mawakin, baya ga tallafin kudi na Naira miliyan 200 da aka ba shi, wanda jimillar kudin ya kai Naira miliyan 315.

Dukku ya ce wannan kyauta ta haifar da tambayoyi daga al’umma kan abubuwan da gwamnatin ta bai wa fifiko.

Ya ce, “Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da jihar ke fama da yara sama da 787,619 da ba sa zuwa makaranta. Da an yi amfani da Naira miliyan 315 wajen mayar da yara sama da 50,000 makaranta ta hanyar shirye-shiryen ilimi na musamman.

“Haka kuma, da za a iya karkatar da wannan kudi zuwa bangarorin kiwon lafiya, gine-ginen more rayuwa, noma, tallafa wa matasa da sauran muhimman ayyukan da za su amfani dubban al’ummar jihar.”

PDP ta kuma zargi gwamnatin Gwamna Inuwa Yahaya da bai wa mawakin filaye guda hudu a Shehu Abubakar District Layout.

Jam’iyyar ta ce wannan mataki abin damuwa ne musamman ganin cewa a baya-bayan nan gwamnati ta rage girman filayen mutane da dama a wannan yanki zuwa rabin abin da suka mallaka ba tare da biyan su diyya ba.

PDP ta ce al’ummar Jihar Gombe na da hakkin sanin dalilan da suka sa aka dauki irin wadannan matakai, tare da yin kira ga gwamnatin jihar da ta fito ta bayyana hujjar da ta dogara da ita wajen rabon wadannan kudade da kadarorin gwamnati.

Sai dai da aka tuntubi Daraktan Harkokin Yaɗa Labarai na Gidan Gwamnatin Jihar Gombe, Ismaila Uba Misilli, ya ce gwamnati ba za ta mayar da martani kan abin da ya bayyana a matsayin zarge-zargen da ba su da tushe daga PDP ba.

A cewarsa, zargin wata dabara ce da PDP ke yi domin ta ci gaba da jan hankalin jama’a da kasancewa cikin harkokin siyasa.

Ya ce, “Ba mu da lokacin ɗaukaka PDP ta hanyar mayar mata da martani kan wannan batu. Wannan wani yunƙuri ne na jam’iyyar da ta rasa tasiri na neman jawo hankali da sake neman muhimmanci a fagen siyasa, musamman yayin da ake tunkarar shekarar zaɓe.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *