Yan Bindiga Sun Bukaci Naira Miliyan 56 Kafin Su Bari a Yi Noma a Zamfara

Lawan Dare, Gwamnan Zamfara

Manoma a yankin Dan Isa, karamar hukumar Kaura Namoda ta jihar Zamfara, sun bayyana cewa ’yan bindiga sun tilasta musu biyan kudade kafin su bari a gudanar da aikin noma a kakar damina ta bana.

Mai unguwar yankin, Malam Hassan Yarima, ya tabbatar da hakan cikin wata tattaunawa ta wayar tarho da Daily Trust, inda ya bayyana cewa kowanne daga cikin kauyuka 35 da ke karkashin jagorancinsa ya biya Naira dubu 800 kafin a amince musu da shiga gonaki.

“Kowane kauye zai sake biyan wasu Naira dubu 800 kafin a bar manoma su girbi amfanin gonarsu. Wannan shi ne yarjejeniyar da muka kulla da jagoran ’yan bindigar da ke wannan yanki, wato Dan Sadiya,” in ji shi.

“Ina magana ne kawai a madadin yankina. Ban san yadda lamarin yake a sauran yankuna ba. Amma abinda na tabbata da shi shi ne: dole ne mutane su biya kudin kafin a bar su su yi noma.”

Malam Yarima ya bayyana cewa ba su da wani zabi illa su bi umarnin ’yan bindigar, domin in ba haka ba za su hana su noma gaba daya.

“Dole ne mu bi dokokinsu. Idan ba mu bi ba, ba za su bar mu mu noma ba. A kalla idan muka yi noma, za mu samu abin da za mu ci da iyalanmu.”

Sai dai, duk da biyansu wannan kudin harajin noma, Yarima ya koka cewa ’yan bindigar na ci gaba da kai farmaki kauyukansu, inda suke sace dabbobi da kwashe kayan abinci.

Ya bayyana cewa mutanen yankin sun riga sun kashe dukiyar da suke da ita wajen kokarin zaman lafiya da ’yan bindigar.

“Muna kokarin zaman lafiya da su, amma gaskiya sun kwashe komai namu. Sun sace dabbobinmu, sun kwashe kudinmu, amfanin gona da sauran kayayyaki.

“Kusan kowane mako sai sun shigo kauyenmu. Kuma duk lokacin da suka zo, dole ne mu tara musu kudi, abinci da kayan masarufi. Wasu lokutan bayan sun kwashe kayan, sai su dauki wasu mata su tafi da su,” in ji shi.