Kociyan kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya, Super Falcons, Justine Madugu, ya samu zabensa a matsayin ɗaya daga cikin ’yan takara na lambar yabo ta Ballon d’Or Women’s Team Coach of the Year na shekarar 2025.
Wannan babban cigaba ne a tarihin kwallon kafar Najeriya, kuma gagarumar nasara ce ga Madugu, wanda ya jagoranci Super Falcons zuwa nasara a gasar cin kofin mata ta Afirka (WAFCON) da aka yi a Maroko.
Shafin hukuma na Ballon d’Or ne ya sanar da wannan zabe a ranar Alhamis, inda sunan Madugu ya shiga sahun manyan masu horaswa na duniya a bangaren kwallon kafa ta mata.
Yanzu haka, Madugu na cikin sahun gwanaye irin su Sarina Wiegman daga Netherlands, Emma Hayes daga Amurka, tsohuwar kociyar Canada Bev Priestman, da Sonia Bompastor, a jerin ’yan takarar lambar yabo ta 2025.
Madugu, mai shekaru 61, ya kawo zaman lafiya da hadin kai a cikin tawagar Super Falcons, inda karkashinsa suka taka leda da kuzari da tsari — suka kuma sake lashe kofin Afirka karo na goma, wanda ya kafa tarihin mafi yawan lashe gasar a nahiyar.
A gasar da aka yi a Maroko, Super Falcons sun lallasa manyan kungiyoyi kamar South Africa, Morocco da Zambia — kungiyoyin da suka hana Najeriya lashe kofin a gasar da ta gabata.
Wannan nasara ba wai kawai ta nuna basirar ‘yan wasan ba ce, har ma ta tabbatar da kwarewa, dabaru da ruhin hadin kai da Madugu ya zubo wa kungiyar.

