Zaben 2027: Zai yi Wahala Kwankwaso ya Mara wa Tinubu Baya – Buba Galadima

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da Buba Galadima

Buba Galadima, babban jigo a jam’iyyar NNPP kuma abokin siyasa na kusa da tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa “zai yi matuƙar wuya” ga Kwankwaso ya haɗa kai da jam’iyyar APC mai mulki domin mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaben 2027.

Galadima ya yi wannan bayani ne a cikin wata hira da gidan talabijin na Channels a shirin Politics Today ranar Litinin, inda ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa Kwankwaso barazana, musamman ta hanyar mara wa Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, baya duk da cewa gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf ta tsige shi.

Da aka tambaye shi ko akwai yiwuwar haɗin gwiwa tsakanin NNPP da APC, Galadima ya ce:
“Gaskiya wannan jita-jita ne nake ji yanzu. Kwankwaso ɗan siyasa ne mai ƙafafunsa. Ku tuna cewa ya fafata da APC a Kano ya kuma kayar da ita. Bai taɓa faɗa min yana shirin goyon bayan Tinubu a 2027 ba.”

Ɗan siyasar mai shekaru ya ƙara da cewa yana fatan sauran ’yan siyasa a Najeriya za su kasance kamar Kwankwaso.

Da aka matsa masa tambaya kan yiwuwar Kwankwaso na tattaunawa a asirce da Tinubu, Galadima ya ce:
“Da akwai wanda ya nemi hakan, da na sani. Ko da ba ni ne mafi kusa da shi ba, a siyasa muna yawan tattaunawa da shi. Bai taɓa faɗa min wani abu makamancin haka ba.”

Ya tambayi yadda za a yi Kwankwaso ya iya haɗa kai da APC “bayan abin da suka yi mana a Kano.”

Ya ce: “An naɗa sarakuna biyu a cikin gari guda? Yanzu akwai sarkin tarayya da sarkin jiha. Wa yake da ikon naɗa sarki da biyan masa albashi?” in ji shi.

Galadima ya zargi gwamnatin tarayya da ɗaukar Aminu Ado Bayero a matsayin sarkinsu na zaɓe saboda zaben 2027. Amma ya ce: “Babu wani sarki a Kano da zai iya shafar yadda mutane za su kada ƙuri’a.”

Ya jaddada cewa mutanen Kano suna da kwarin gwiwa ga Kwankwaso saboda sun ga ayyukansa a kasa: “Shi ya sa suke binsa a siyasa,” in ji shi.

Game da matsayin NNPP a 2027, Galadima ya ce ba a yanke hukunci na ƙarshe ba tukuna, amma ya tabbatar da cewa:
“Inda kuka tarar da mu, a can ne za a kafa gwamnati.”