Trends

Yan Sanda Sun kama Bogin Dan Sanda da Bindiga a Katsina

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Katsina ta kama wani mutum mai suna Mubarak Bello, mai shekaru 38, bisa zargin mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba da kuma yin karyar ƴan sanda da mukamin AD Asst.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Abubakar Aliyu, ya fitar a ranar Lahadi a madadin kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Bello Shehu.

Aliyu ya bayyana cewa jami’an tsaro sun cafke wanda ake zargi ne yayin sintiri da misalin ƙarfe 2:30 na safe ranar Asabar, bayan sun lura da motsin da ya tada musu hankali.

“A ranar 13 ga Satumba, 2025, da misalin ƙarfe 02:30 na safe, jami’an da ke sintiri daga sashen ayyuka na rundunar sun samu nasarar cafke Mubarak Bello, ɗan asalin unguwar Kofar Yamma a karamar hukumar Kurfi, bisa zargin mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba da kuma karyar ƴan sanda,” in ji sanarwar.

Aliyu ya ƙara da cewa an tsayar da wanda ake zargin ne yana tukin motar Toyota Corolla, ash, mai lambar Lagos GGE 473 BH, amma bai iya ba da cikakken bayani kan kansa ko motar ba.

A cewar sanarwar:

“Binciken da aka yi a cikin motar ya haifar da gano wasu kayayyaki masu haɗari, waɗanda suka haɗa da: bindiga kirar gida guda ɗaya, harsasai guda huɗu, harsasai da aka yi amfani da su guda biyu, katin shaida na bogi na ƴan sanda, da ƙarin faranti na lamba daga Kano (FGE 68).”

Rundunar ta ce ana ci gaba da tsare wanda ake zargin yayin da ake zurfafa bincike domin gano yadda ya samu makamin da katin bogi da sauran kayayyakin.

“Wanda ake zargi yana tsare a hannunmu yayin da ake zurfafa bincike. Za a sanar da ƙarin bayani ga jama’a a nan gaba,” in ji Aliyu.