Hukumar Lafiya ta Duniya, World Health Organization (WHO), ta bukaci gwamnatoci da su saka bukatun ‘yan gudun hijira da ‘yan ci-rani cikin manufofi, dabaru da tsare-tsaren kiwon lafiya na kasa.
“Tsarin kiwon lafiya ba zai zama na kowa ba sai ya yi hidima ga kowa,” in ji Darakta Janar na WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Wani sabon rahoto na WHO ya nuna babban sauyi a yadda kasashe ke mayar da martani, inda fiye da kasashe 60 — kusan kashi biyu cikin uku na wadanda aka bincika — yanzu sun hada ‘yan gudun hijira da ‘yan ci-rani a cikin dokoki da manufofinsu na kiwon lafiya.
Rahoton ya kafa matakin farko na duniya wajen bibiyar ci gaban samar da tsarin kiwon lafiya mai hada kowa da kuma mai kula da bukatun ‘yan ci-rani.
“‘Yan gudun hijira da ‘yan ci-rani ba kawai masu karbar kulawa ba ne, su ma ma’aikatan lafiya ne, masu kula da marasa lafiya, da shugabannin al’umma,” in ji Ghebreyesus, yana mai jaddada cewa hada su a tsarin yana kara karfin shirin fuskantar kalubalen lafiya na gaba.
WHO ta ce zuba jari a lafiyar ‘yan gudun hijira na kawo fa’ida ta hanyar taimakawa hadewa da jama’a da kuma karfafa tsaron lafiyar duniya.
Misalan kasashe sun nuna ci gaba: Thailand ta fadada inshorar lafiya ga ‘yan ci-rani, Belgium na amfani da masu fassara da masu sulhu na al’adu daban-daban, yayin da Chile ke hada wakilan ‘yan ci-rani a yanke shawarar kula da lafiya a matakin farko.
WHO ta ce wadannan misalai na nuna yadda hujjoji da kimiyya ke jagorantar gyare-gyare ko da a yanayin siyasa mai sarkakiya.
Sai dai har yanzu akwai gibi. Kashi 37 cikin 100 na kasashe ne kawai ke tattara bayanan lafiya masu alaka da ‘yan ci-rani akai-akai, kashi 42 cikin 100 ne ke hada su a tsare-tsaren gaggawa, kuma kasa da kashi 40 cikin 100 ne ke horas da ma’aikatan lafiya kan kula da marasa lafiya bisa fahimtar al’adu. Haka kuma, kashi 30 cikin 100 ne kacal suka kaddamar da kamfen din yaki da wariya.
WHO ta bayyana cewa sama da mutane biliyan daya — wato mutum daya cikin takwas a duniya — na rayuwa a matsayin ‘yan gudun hijira ko ‘yan ci-rani, inda galibi suke fuskantar kalubalen samun kulawa, karin hadarin kamuwa da cututtuka, da kuma yanayin rayuwa marasa tsaro.
“Tsarin kiwon lafiya mai hada kowa da kuma mai la’akari da ‘yan ci-rani yana rage kashe kudade a nan gaba ta hanyar samar da al’umma masu lafiya da suka hada kai, wadanda za su bayar da gudunmawa sosai ga ci gaban kasa,” in ji hukumar.
Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta kuma bukaci gwamnatoci, abokan hulda da masu bayar da tallafi su kara kaimi wajen cimma wannan buri.
“Ta hanyar saka ‘yan gudun hijira da ‘yan ci-rani cikin dabarun kiwon lafiya na kasa, kasashe za su iya kara juriya, inganta sakamako, tare da tabbatar da cewa ba a bar kowa a baya ba,” in ji WHO.

