Trends

UNYC Ta Jaddada Kudirin Ƙarfafa Jagorancin Kishin Kasa Don Cigaba

Kungiyar UNYC yayin babban taron su a Abuja

Ƙungiyar United Nigerian Youths Congress (UNYC) ta sake nanata kudirinta na gina amana, ƙarfafa wayewar ƙasa, haɗin kai da jagorancin kishin ƙasa a fadin Najeriya domin tabbatar da cigaban ƙasa.

Ƙungiyar ta bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin Taron Matasa na 2025 mai taken “Nigeria First: Leadership Solutions for National Growth”, wanda aka gudanar a Hotel Nicon Luxury, Abuja.

Shugaban ƙungiyar, Arc. Bashir Chambers, ya ce taron ya zama abin tunawa a yayin da ake ci gaba da yin ƙoƙari wajen cika burin mahalarta kafa Najeriya.

Ya ce, “A yau mun kaddamar da sabon salo, rana da za ta kasance tarihi a cikin tarihin ƙasarmu. Mun cika burin kakanninmu wajen gina ƙasa ɗaya mai adalci da gaskiya.”

Chambers ya ƙara da cewa, “United Nigerian Youths Congress na tsaya gaban ƙasa ba a matsayin ƙungiyar matsin lamba ba, ko masu kallo a cikin tsarin dimokuraɗiyya ba, sai dai a matsayin shugabanni, masu tsara manufofi, da masu rike da amanar sabuwar Najeriya.”

A nasa jawabin, Dr. Hakeem Ahmed, wanda ya yi jawabi a taron, ya jaddada muhimmancin zuba jari a kan matasan Najeriya.

Ya ce, “Ga matasan da ke nan, kun zama ginshiƙan komai, domin ba tare da matasa masu kishin ƙasa ba, babu wata ƙasa.”

Ahmed ya bayyana cewa, akwai nauyin da ya rataya a wuyan manyan mutane wajen tallafawa matasa, yana mai cewa:

“Akwai buƙatar mu zauna da ku, mu horar da ku, mu karfafa ku, mu ba ku abin da kuke bukata, mu kula da mafita domin gina Najeriya mai arziki.”

Taron ya mayar da hankali kan inganta kishin ƙasa da haɗin kai, inda ya tattaro wakilai daga sama da ƙungiyoyin fararen hula (CSOs) 1000, domin ƙarfafa daɗaɗɗen haɗin kan ƙasa da cigaba.

Babban abin da ya ƙayatar a taron shi ne rattaba hannu kan Takardar Fahimtar Juna (MoU) mai taken: “COALITION FOR A NEW NIGERIA: Unity, Peace & Patriotism” da dukkan CSOs da suka halarta suka sanya hannu a kai.