Trends

Ministan Tsaro: Tinubu Ya Nemi Yan Majalisa da su Tantance Tsohon CDS Musa

Bola Ahmed Tinubu Shugaban kasar Nigeriya

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon Ministan Tsaro, kamar yadda sanarwar da Bayo Onanuga, Mai Ba da Shawara na Shugaba (Bayanai da Tsare-tsare), ya fitar.

A cikin wasika da ya aikawa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Shugaba Tinubu ya bayyana nadin Janar Musa a matsayin magajinsa Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, wanda ya resign ranar Litinin.

Janar Musa, mai shekaru 58, babban soja ne wanda ya yi aiki a matsayin Shugaban Rundunar Tsaro daga shekarar 2023 har zuwa Oktoba 2025. Ya lashe kyautar Colin Powell na Soja a shekarar 2012.

Shugaba Tinubu ya nuna cikakken tabbaci game da iya jagorancin Janar Musa a Minsitirin Tsaro da kuma kara inganta tsarin tsaro na Najeriya.

Nadin Janar Musa yana bukatar amincewar Majalisar Dattawa.