Kungiyar Women in Public Health Leadership for Africa (WiPHLA) ta kaddamar da ayyukanta domin karfafa gudunmuwar mata a fannin lafiyar jama’a a nahiyar Afrika, tare da nufin inganta tsarin kiwon lafiya da samar da kyakkyawan sakamakon lafiya.
Shirin ya yi niyya ne wajen kara tasiri da wakilcin mata musamman a manyan mukaman shugabanci a bangaren lafiyar jama’a a nahiyar.
An gudanar da taron ne a dakin taro na Shehu Yar’Adua Centre da ke Abuja, karkashin taken: “Catalyzing and Amplifying Leadership Effectiveness for Women in Public Health Leadership.”
Dr. Bolanle Oyeledun, mamba a majalisar gudanarwa ta WiPHLA, ta bayyana taron a matsayin tarihi da kuma sabon salo na cigaba.
Ta ce mata suna da kaso mai yawa a aikin kiwon lafiya a nahiyar Afrika.
“Wannan rana ce ta tarihi sosai. Mun dauki babban mataki a ci gaban shugabancin lafiyar jama’a a nahiyarmu, kuma ina alfahari kasancewa cikin wannan motsi,” in ji ta.
Ta kara da cewa dole ne a baiwa mata kayan aiki da kwarewa domin rike mukaman jagoranci.

“Ba za a samu dorewar ingantaccen sakamakon lafiya a Afrika ba matuqar ba mu hada kai wajen karfafa mata da ke zama ginshikin tsarin kiwon lafiya ba,” ta bayyana.
Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Dr. Hadiza Balarabe, ta yi tsokaci iri ɗaya, inda ta kawo misalan yadda mata suka taka muhimmiyar rawa a harkar lafiya a jiharta.
Ta ce binciken duniya ya nuna cewa shugabanci mai daidaiton jinsi yana haifar da nagartaccen gudanarwa, ƙarfi ga cibiyoyi, da ingantaccen sakamakon lafiya.
“Binciken Harvard School of Public Health ya nuna cewa ƙungiyoyin da suka daidaita tsakanin mace da namiji a shugabanci suna da kyakkyawan tsarin tafiyar da aiki da juriya. Ana samun gibin aiki idan shugabanci bai wakilci al’ummar da yake yi wa hidima ba,” in ji ta.
Dr. Balarabe ta bayyana abubuwa uku da suke da muhimmanci wajen inganta matakin jagorancin mata a lafiyar jama’a: gina kwarewa, bunkasa jagoranci, da tasiri.
Wakilin Ofishin Jakadancin Faransa, Pierre-Louis Bonnel, ya nuna goyon bayan kasarsa ga shirin, yana mai jaddada muhimmancin jagorancin mata a fannin lafiyar jama’a.
“Muna farin cikin ganin irin wannan hazakar shugabanci da aka nuna yau – da jajircewa, kirkira, da kokarin hada dukkan abubuwan da ake bukata a Najeriya da wajen ta,” in ji shi.
Ya kara da cewa Faransa na goyon bayan duk wani yunkuri da ke da alaka da inganta mata ko da yaushe, a kowanne fanni.
