Tinubu ya Yafe wa Mamman Vatsa, Farouk Lawan da Wasu Wutane 173

Bola Ahmed Tinubu Shugaban kasar Nigeriya

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bai wa mutane 175 afuwa da sassauci na musamman, ciki har da afuwar mutuwa (posthumous pardon) ga marigayi Manjo Janar Mamman Jiya Vatsa da kuma gwarzon kishin kasa Herbert Macaulay.

Wannan mataki ya biyo bayan amincewar Majalisar Koli ta Kasa (National Council of State) da ta gudanar da taronta a ranar Alhamis a Abuja.

A cewar wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Bayani da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya fitar, shugaba Tinubu ya kuma bai wa tsohon dan majalisa Farouk Lawan da wasu uku Mrs. Anastasia Daniel Nwaobia, Barrister Hussaini Umar, da Ayinla Saadu Alanamu afuwa bayan an tabbatar sun nuna nadama da kuma shirin komawa cikin al’umma da halin kirki.

Marigayi Manjo Janar Mamman Vatsa, wanda aka kashe a shekarar 1986 bayan kotu ta same shi da laifin cin amanar kasa, ya samu wannan afuwa bayan kusan shekaru arba’in da rasuwarsa.

Haka kuma, Herbert Macaulay, daya daga cikin fitattun ‘yan kishin kasa na farko a Najeriya kuma wanda ya kafa NCNC (National Council of Nigeria and the Cameroons), ya samu afuwa bisa abin da aka bayyana a matsayin hukuncin da ba daidai ba da gwamnatin mulkin mallaka ta yanke masa a shekarar 1913.

Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa Shugaba Tinubu ya bai wa fursunoni 82 afuwa kai tsaye, ya rage wa mutane 65 zaman gidan yari, sannan ya mayar da hukuncin kisa na mutane 7 zuwa daurin rai da rai.

Bugu da ƙari, shugaban kasa ya bai wa mutane tara na Ogoni (Ogoni Nine) da aka kashe a shekarar 1995 Ken Saro-Wiwa, Saturday Dobee, Nordu Eawo, Daniel Gbooko, Paul Levera, Felix Nuate, Baribor Bera, Barinem Kiobel, da John Kpuine — afuwar mutuwa (posthumous pardon).

Ya kuma ba wasu gwarzaye hudu lambar yabo ta kasa bayan mutuwarsu, wadanda suka hada da: Chief Albert Badey, Chief Edward Kobani, Chief Samuel Orage, da Theophilus Orage.

Wannan aikin ya samo asali ne daga shawarwarin Kwamitin Shugaban Kasa kan Hakkin Afuwa (Presidential Advisory Committee on the Prerogative of Mercy – PACPM), wanda Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi (SAN) ke jagoranta.

Kwamitin ya duba shari’u 294, inda ya bada shawarar:

Bai wa fursunoni 82 afuwa,

Afuwar cikakke ga mutane 2,

Rage wa mutane 65 hukuncin zaman gidan yari,

Mayar da hukuncin kisa na mutane 7 zuwa daurin rai da rai,

Da kuma afuwar mutuwa ga mutane 15, ciki har da Ogoni Nine.

Ka’idojin da aka yi amfani da su wajen bayar da afuwar sun hada da shekaru (60 da sama), rashin lafiya mai tsanani, matasa (16 da kasa), halin kirki a cikin gidan yari na dogon lokaci, da nuna nadama.

A watan Janairu 2025, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ne ya kaddamar da wannan kwamiti domin inganta adalci, gyaran hali, da kare hakkin dan Adam a Najeriya.