Trends

Tinubu ga ‘Yan Najeriya: Hakuri da Jimrewa Ita ta Haifar da Cigaba da Bunƙasa

Bola Ahmed Tinubu Shugaban kasar Nigeriya

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa ‘yan Najeriya bisa juriyarsu da haƙurinsu a cikin matsalolin tattalin arziki da zamantakewa na baya-bayan nan, yana tabbatar da cewa hadayunsu ba a banza suke ba, domin tuni sun fara haifar da cigaba da bunƙasa.

Da yake jawabi a ranar Juma’a a wurin bikin naɗin Sarki na 44 na Ibadanland, Oba Rashidi Ladoja, a filin tarihi na Mapo Hall da ke Ibadan, Shugaban Ƙasa ya jinjinawa juriya da haƙurin jama’a a cikin mawuyacin hali, tare da yin alkawarin cewa kwanaki masu kyau suna gabatowa.

Ya ce:

“Na sani cewa lokaci yana da wahala, amma wahalar da kuke sha ba ta tafi a banza ba. Hanyar da muke bi tuni ta fara haifar da ‘ya’yan cigaba, kuma ina tabbatar muku cewa muna shimfiɗa harsashin gina kyakkyawar makoma mai albarka da walwala.”

Yayin da yake jawabi ga taron manyan sarakunan gargajiya, shugabannin siyasa da jama’a, Shugaban Ƙasa ya yaba wa Oba Rashidi Ladoja, yana bayyana shi a matsayin “sarki mai hikima, zaman lafiya da hangen nesa.”

Tinubu ya tuna da kalubalen da Ladoja ya fuskanta lokacin yana gwamna wanda ya kai ga sauke shi daga mulki, yana mai cewa yana farin ciki da dawowarsa.

Ya ce:

“Ina mika gaisuwar ban girma ga Mai Martaba Oba Rasidi Adewolu Ladoja Arusa na ɗaya. Da sauran sarakunan gargajiya baki ɗaya.
Wannan rana babbar rana ce a tarihi, kuma ina farin cikin kasancewa cikin wannan tarihi na nadin ka. Yana da daraja a gare ni.”

LShugaban Ƙasa ya kuma gaishe da tsoffin gwamnoni Donald Duke, Olagunsoye Oyinlola da Gbenga Daniel, yana mai cewa wannan lokaci ba na dogon jawabi ba ne.

Ya ƙara da cewa:

“Kabiyesi Oba Rashidi Ladoja ba wai mutum ne kawai mai dimbin kwarewa ba ne, amma mutum ne da al’ummarsa ke matuƙar ƙauna. Hawansa gadon sarauta ya buɗe sabon babi na fata da haɗin kai ga Ibadanland. Ba ni da wata shakka cewa ƙarƙashin jagorancinsa, Ibadan za ta shaida cigaba mai girma.”

Tinubu ya sake nanata kudirinsa na yin aiki tare da majalisun gargajiya da gwamnatocin jihohi domin tabbatar da zaman lafiya, tsaro da farfaɗo da tattalin arziki a fadin ƙasar.