Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da sabbin kuɗin aikin Hajji na shekarar 2026, inda alhazai za su biya tsakanin Naira miliyan 8.1 zuwa Naira miliyan 8.5, gwargwadon yankin da suka fito.
Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ne ya bayyana haka bayan rattaba hannu kan yarjejeniyoyi da kamfanonin ba da hidima a Masarautar Saudiyya.
A cikin wata sanarwa daga sashen yada labarai na hukumar, an ce:
“Bayan tattaunawa da dukkan masu ruwa da tsaki, ciki har da shugabannin jihohi da samun amincewar Gwamnatin Tarayya, Shugaban/CEO na Hukumar Alhazai ta Ƙasa, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, yana sanar da kuɗin aikin Hajjin 2026 kamar haka:
Yankin Maiduguri-Yola (jihohin Yobe, Borno, Adamawa da Taraba) – ₦8,118,333.67
Sauran jihohin Arewa – ₦8,244,813.67
Jihohin Kudu – ₦8,561,013.67.”
Sanarwar ta ƙara da cewa, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, wannan sabon farashi ya ragu da matsakaitan Naira 200,000 ga kowanne mahajjaci.
Tawagar NAHCON da ke kasar Saudiyya ta rattaba hannu kan yarjejeniya da Kamfanin Hidimar Hajji na 2026 (Mashareeq Al-Zahabiyya) da kuma Kamfanin Sufuri (Daleel Al-Ma’aleem).
Farfesa Usman ya shawarci dukkan masu niyyar zuwa Hajji su tabbatar sun kammala biyan kuɗin su kafin 31 ga Disamba, 2025.
