Ministan Ayyuka, Dave Umahi, ya bayyana cewa yankin Kudu maso Gabas, musamman jihar Ebonyi, zai mara baya ga Shugaba Bola Tinubu a zaben shugaban kasa na 2027, tare da watsar da tasirin ƙungiyar OBIdient da Peter Obi ke jagoranta a yankin.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da farin jinin Peter Obi ke ƙara ƙaruwa a siyasar Najeriya, musamman a tsakanin matasa.
Da yake jawabi a ranar Asabar yayin bikin Ohanivo 2025 New Yam Festival a ƙaramar hukumar Onicha, jihar Ebonyi, Umahi ya jaddada cewa Kudu maso Gabas ba ta cikin tafiyar OBIdient a yanzu, yana mai cewa shekaru na wariya a siyasa sun sa yankin ya sauya salon siyasa.
A cewarsa:
“Ba mu OBIdient ba. An yi mana wulakanci sosai a siyasa har muka daina kasancewa OBIdient. A’a, ba mu ba.
“Amma mutumin da ya ba mu jin daɗin kasancewa cikin ƙasa, shi ne Shugaba Bola Tinubu. Kada a ce mu daga Ebonyi amma muna cewa wannan jiha ba ta da OBIdient. Babu ɗan OBIdient a Ebonyi.”
Tsohon gwamnan Ebonyi ya jaddada cewa Shugaba Tinubu ya nuna alheri ga yankin Kudu maso Gabas, kuma su ma za su saka masa a zaben 2027.
Ya ce mutanen yankin sun waye a siyasa kuma ba za su sake bari a yaudare su ba, yana nuni da sakamakon zaben shugaban kasa na 2023 a matsayin kuskure.
Umahi ya ƙara da cewa:
“Abin da ya kamata mu yi shi ne mu lissafa abubuwan alherin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Kudu maso Gabas da jihar Ebonyi a lokacin da ya dace. Ba za mu sake bari a yaudare mu ba, domin zaben da ya gabata kuskure ne, amma yanzu mun waye. Ba zan iya kammala jerin ayyukan da Shugaban ke yi mana ba.”
