Kafin taron kwamitin zartarwa na kasa (National Executive Committee – NEC) na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da za a gudanar a ranar 25 ga watan Agusta, shugabancin jam’iyyar ya duba ayyukan da ke saba wa manufofin jam’iyya da wasu mambobinta suka aikata, tare da kammala shirye-shiryen daukar matakan ladabtarwa a kan su, a shirye-shiryen jam’iyyar na fuskantar zaben 2027.
Hukuncin na iya zama wani bangare na tattaunawar da ake yi da wasu fitattun shugabannin jam’iyyun adawa, ciki har da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaben 2023, Peter Obi, domin shigowa PDP.
Majiyar ta ce, shugabancin PDP na mayar da hankali ne kan mambobin da suka riga suka nuna goyon bayansu ga sake tsayawar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, na daga cikin fitattun mambobin PDP da suka sha bayyana goyon bayan su ga Tinubu, duk da cewa shugaban kasar bai bayyana aniyarsa ta neman wa’adi na biyu ba tukuna.
Ko da yake Wike na cikin PDP wacce jam’iyyar adawa ce, amma shi minista ne a gwamnatin Shugaba Tinubu na jam’iyyar mai mulki, All Progressives Congress (APC).
Kwanan nan, tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya shiga tare da mambobin APC na jiharsa wajen bayyana goyon bayan Tinubu a zaben 2027, duk da cewa ya sanya hular PDP a wurin taron a matsayin alamar cewa har yanzu yana cikin jam’iyyar.
Haka zalika, kimanin makonni biyu da suka gabata, gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, da wasu mambobin PDP na jihar sun bayyana Tinubu a matsayin dan takarar su na shugaban kasa a zaben 2027.
A cikin wata sanarwa mai zafi da aka fitar ranar Juma’a, mai magana da yawun PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya bayyana cewa lamarin na da matukar damuwa ga jam’iyya.
Haka kuma, shugaban riko na yankin Kudu-Maso-Kudu na PDP, Emmanuel Ogidi, ya bayyana cewa kwamitin zartarwa na kasa (National Working Committee (NWC) zai sake duba ayyukan Wike kuma zai yanke hukunci a mako mai zuwa.









