Pate Ya Yabi Jihar Plateau Kan Gyaran Fannin Kiwon Lafiya

Ministan Lafiya Farfesa Mohammed Ali Pate

Ministan Lafiya da Jin Ƙai na Tarayya, Farfesa Muhammad Pate, ya yaba wa Gwamnatin Jihar Plateau kan ƙoƙarinta na inganta isar da ayyukan kiwon lafiya na matakin farko a jihar.

Pate ya yi wannan yabon ne a Jos a wajen bikin yaye rukunin farko (Cohort 1.0) tare da karɓar sabon rukuni na biyu (Cohort 2.0) na Shirin Ƙwararrun Lafiya na Ƙasa (National Health Fellows) a Plateau.

Ministan ya ce ƙididdiga sun nuna cewa Plateau na samun gagarumin ci gaba a fannin kiwon lafiya na farko ta hanyar farfaɗo da cibiyoyi, tallafin kasafin kuɗi, da samar da inshorar lafiya ga al’umma masu rauni.

Pate, wanda Dakta Pokop Bupwatda, Babban Daraktan Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH) ya wakilta, ya ce jihar na kuma ƙarfafa tsarin tsare-tsare da haɗin gwiwa domin mayar da hankali kan lafiyar iyaye mata, jarirai da yara.

Ya ƙara da cewa a Taron Majalisar Lafiya ta Ƙasa na 2025, Plateau ta jagoranci aiwatar da shawarwarin da aka cimma a taron 2024, wanda ya ce hakan ya samu ne sakamakon ƙarfin gwiwar siyasa da aka nuna.

A cewarsa, a watan Afrilun 2024, Shugaba Bola Tinubu ya amince da Shirin Ƙwararrun Lafiya na Ƙasa (NHFP) domin inganta samun kulawar lafiya mai inganci a Najeriya.

Ya ce shirin ya zaɓo matasa masu kishin ƙasa daga dukkan ƙananan hukumomi 774 na ƙasar, inda ake gina musu ƙwarewa domin kawo sauyi mai amfani a al’ummominsu.

“NHFP alama ce ta sabuwar Najeriya inda baiwa da ƙwarewa ke bai wa matasa damar kaiwa ga cikakken burinsu.

“A tsawon shekarar shirin, mambobin rukuni na farko a Plateau da sauran wurare sun yi aiki tare da al’ummominsu da ƙungiyoyin lafiya domin inganta haɗin kai, amfani da bayanai, yaƙi da cututtukan mata masu juna biyu da yara, magance shan miyagun ƙwayoyi, da sake gina amincewa da ayyukan lafiya.

“Ƙarfin gwiwarsu da sababbin dabaru sun ƙarfafa gyare-gyaren da ake yi domin inganta isar da ayyukan lafiya,” in ji shi.

Ya kuma ƙarfafa sabbin mambobin rukuni na biyu da su gina kan tubalin da rukuni na farko ya kafa tare da nuna ƙwarewa da jajircewa.

“Kun fara tafiyarku ne a lokacin da tsarin lafiya ke buƙatar ƙarin amfani da bayanai a kowane mataki, zurfafa haɗin kai tsakanin al’umma da ma’aikatan lafiya, samar da mafita ga ƙalubalen isar da sabis, da kuma mayar da hankali kan lafiyar mata da jarirai,” in ji shi.

Haka zalika, Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya ce shirin NHFP a jihar ba kawai tsari ba ne, illa motsi ne na ƙarfafawa, jagoranci da hidima.

Mutfwang, wanda mataimakiyarsa, Misis Josephine Piyo ta wakilta, ya ce shirin ya daidaita jihar da manufofin sabunta dabarun zuba jari a fannin lafiya na Gwamnatin Tarayya da kuma Ajandar Sauya Kiwon Lafiya na Farko.
Ya ce hakan zai tabbatar da cewa Plateau ba ta baya ba, sai dai tana tafiya tare da sauran jihohi wajen shiga sabon zamani na gyaran fannin lafiya.

Tun da farko, Kwamishinan Lafiya na Jihar Plateau, Dakta Nicholas Ba’amlong, ya ce bikin yaye da karɓar sababbin mambobin na nuna ƙudurin jihar na ƙarfafa tsarin lafiyarta da ma na ƙasa baki ɗaya.

“Jihar ta rungumi wannan hangen nesa gaba ɗaya, tana gane cewa lafiyar al’umma ita ce ginshiƙin duk wani ci gaba,” in ji shi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa duka rukunan biyu sun ƙunshi mutane 17-17, waɗanda aka zaɓo daga ƙananan hukumomi 17 na jihar.