Tinubu Ya Naɗa Farfesa Amupitan a Matsayin Shugaban Hukumar Zaɓe (INEC)
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) a matsayin sabon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC). Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis. A cewar Onanuga, Majalisar Ƙasa ta Koli (National…
