Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da shirin kawo karshen dogaro da tallafin kasashen waje wajen yaki da cututtukan HIV da tarin fuka nan da shekarar 2030, tare da karkata zuwa amfani da kudaden cikin gida.
Ministan Lafiya mai kula da ayyukan hadin gwiwa, Muhammad Ali Pate, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin kaddamar da Tsarin Bibiyar Ayyuka na Bangarori da dama kan tarin fuka da kuma sabon maganin rigakafin HIV mai allura mai dadewa (PrEP).
“Muna son daina dogaro da tallafin waje a hankali. Nan da 2030, ya kamata Najeriya ta iya amfani da nata kudaden cikin gida wajen magance manyan cututtukan da ke addabar al’ummarta,” in ji Pate, yana mai nuni da cewa kudaden tallafin lafiya daga kasashen waje na raguwa.
Ya bayyana cewa tuni gwamnati ke kara yawan kudaden da take warewa a kasafin kudi tare da karfafa tsarin bin diddigi da gaskiya domin tabbatar da dorewar shirye-shiryen, yayin da ake aiki tare da jihohi da abokan hulda domin maye gurbin tallafin waje a hankali.
Karamin Ministan Lafiya, Iziak Salako, ya ce kaddamarwar abubuwa biyu a lokaci guda na nuna sabon salo na hadaka da kirkire-kirkire a tsarin kiwon lafiya.
Ya bayyana sabon maganin rigakafin HIV mai allura a matsayin babban ci gaba, musamman ga mutanen da ke fuskantar wariya ko kuma ke da wahalar shan magani kullum.
Babbar Sakatare a ma’aikatar, Daju Kachollom, ta kara da cewa taron ya nuna manyan nasarori biyu: fara amfani da maganin rigakafin HIV mai dadewa a fadin kasa da kuma gabatar da tsarin bibiyar ayyuka kan tarin fuka.
Ta ce ma’aikatar na da kudurin fadada ayyukan sa ido, gano cuta, da kuma gwaje-gwajen al’umma domin dakile yaduwar cututtuka.
Najeriya na daya daga cikin kasashen da ke da yawan masu dauke da cutar HIV a duniya na biyu, inda kimanin mutane miliyan 1.9 ke rayuwa da cutar.
Duk da cewa yawan kamuwa da cutar ya ragu, masana sun yi gargadi cewa rigakafi na ci gaba da kasancewa rauni, musamman saboda kalubalen wariya da kuma wahalar bin tsarin shan maganin PrEP na baka akai-akai.
