Trends

ADC ta yi Maraba da Kwankwaso, ta Nemi Haɗin Kan Yan Jam’iyya

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso babban jigo a jam’iyyar NNPP

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta yi maraba da tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, tare da magoya bayansa cikin jam’iyyar, inda ta bayyana hakan a matsayin wani muhimmin mataki ga dimokuradiyyar Najeriya.

Shugaban jam’iyyar na ƙasa, David Mark, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, inda ya ce shigar Kwankwaso cikin ADC tare da “miliyoyin magoya baya” wata manufa ce ta shugabannin adawa domin haɗa kai da ƙarfafa harkokin dimokuraɗiyya a ƙasar.

Ya ce wannan mataki na nuna yadda jam’iyyun adawa ke amsa kiran da ‘yan Najeriya ke yi na samar da haɗin kai domin kare tsarin dimokuraɗiyya.

Mark ya soki jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yana mai zargin cewa ayyukanta na barazana ga tsarin jam’iyyu da dama, tare da gargadin cewa akwai yunƙurin raunana muryoyin adawa da kuma tara iko a wuri guda.
A cewarsa, faɗaɗar haɗin gwiwar ADC na nuna aniyar tabbatar da cewa ‘yan Najeriya suna da damar zaɓar shugabanninsu cikin gaskiya da adalci.

“Ba za a gina makomar Najeriya ta hanyar danniya ba; dole ne a gina ta ta hanyar ba kowa dama,” in ji shi, yana mai ƙara da cewa dole ne shugabanci ya samu ne ta hanyar amincewar jama’a, ba ta hanyar iko kawai ba.

Mark ya kuma bayyana ADC a matsayin “tushen wata sabuwar tafiya ta ƙasa” wadda ta mayar da hankali kan haɗin kai, gaskiya da kuma shugabanci mai kula da bukatun jama’a.

Ya yi kira ga ‘yan Najeriya daga kowane yanki, addini da jam’iyya da su haɗa kai da wannan tafiya, yana mai jaddada muhimmancin haɗin kai wajen magance ƙalubalen ƙasa.

Haka kuma, shugaban ADC ya gayyaci sauran jam’iyyun siyasa, ƙungiyoyin farar hula da kuma matasa da su shiga wata babbar haɗaka domin ƙarfafa dimokuraɗiyya da inganta shugabanci a ƙasar.

Ya ce wannan lokaci ya kamata ya zama wani sabon babi a siyasar Najeriya, yana kira ga ‘yan ƙasa da su rungumi haɗin kai da aiki tare domin gina makomar ƙasa.