Hukumar Tara Kuɗaɗen Shiga ta Najeriya, Nigeria Revenue Service (NRS), ta bayyana cewa kuɗaɗen da aka tara daga Harajin Ribatar Jari (Capital Gains Tax – CGT) sun kai tarihin Naira biliyan 522 a shekarar 2025, adadin da ya zarce hasashe da kashi 869 cikin ɗari na abin da aka sa a gaba.
Daraktar Zartarwa mai kula da Harkokin Gwamnati da Manyan Masu Biyan Haraji, Amina Ado, ce ta bayyana hakan a taron ja da baya na shugabannin hukumar (Management Retreat) da aka gudanar a Abuja. Ta ce kuɗaɗen sun tashi daga Naira biliyan 52 a 2024 zuwa Naira biliyan 522 a 2025 — ƙarin Naira biliyan 470 cikin shekara guda.
Rahoton ya danganta wannan gagarumin ƙaruwa da sayar da kadarori (divestments) da kamfanonin mai da iskar gas na matakin sama (upstream) suka yi, lamarin da ya nuna yadda ake sake fasalin kasuwanci da sayar da kadarori a fannin.
Takardar gabatarwar ta ce, “Babban kuɗin CGT ya samo asali ne daga sayar da kadarori da kamfanonin mai da iskar gas na upstream suka yi.”
Harajin Ribatar Jari na shafar ribar da aka samu daga sayar da kadarori kamar filaye, gine-gine, hannayen jari, jarin kasuwanci, da kadarorin dijital.
Sauye-sauyen Haraji
Sabbin gyare-gyare sun ɗaga harajin CGT ga manyan kamfanoni daga kashi 10 cikin ɗari zuwa kashi 30 cikin ɗari, daidai da harajin kuɗin shiga na kamfanoni. Ga daidaikun mutane kuwa, ana cajin harajin bisa matakin harajin kuɗin shigar da suka dace da shi.
Haka kuma, gwamnati ta ƙara iyakar kuɗin da ba za a biya haraji ba kan sayar da hannayen jari a kamfanonin Najeriya zuwa Naira miliyan 150 a shekara, muddin ribar ba ta wuce Naira miliyan 10 ba. Ana sa ran wannan mataki zai keɓe sama da kashi 99 cikin ɗari na masu zuba jari daga biyan CGT.
Sai dai, Association of Securities Dealing Houses of Nigeria (ASHON) ta yi gargaɗin cewa sabon tsarin harajin na iya rage kwarin gwiwar masu zuba jari.
A gefe guda, Shugaban Kwamitin Gyaran Haraji na Fadar Shugaban Ƙasa, Taiwo Oyedele, ya ce daidaita CGT da harajin kamfanoni zai ƙara darajar kamfanoni da kuma samar da alfanu na dogon lokaci.
Oyedele ya bayyana cewa ƙananan ‘yan kasuwa da masu ƙaramin karɓar albashi ba za su fuskanci wannan haraji ba. Ya ce, “Idan ƙaramin kamfani na biyan sifili cikin ɗari na harajin kamfanoni, to harajin ribatar jarinsa ma sifili ne. Haka kuma, masu ƙaramin albashi da aka keɓe daga harajin PAYE ba za su biya harajin ribatar jari ba.”
