Trends

Nigerian Breweries Ta Samu Kuɗaɗen Shiga Naira Tiriliyan 1.467 a 2024

Kamfanin Nigerian Breweries Plc ya sanar da samun kuɗaɗen shiga na Naira tiriliyan 1.467 a shekarar 2024, wanda ya nuna ƙaruwa da kashi 35 cikin ɗari idan aka kwatanta da Naira tiriliyan 1.08 da aka samu a 2023. Hakan na ƙunshe ne cikin rahoton kuɗaɗen da aka tantance kuma aka miƙa wa Nigerian Exchange Limited (NGX).

Kamfanin ya farfaɗo daga ƙalubalen da ya fuskanta a 2023, inda ribar ɗanyen kaya (gross profit) ta ƙaru da kashi 77 cikin ɗari zuwa Naira biliyan 565.18, idan aka kwatanta da Naira biliyan 319.92 a shekarar da ta gabata.

Sai dai kuɗin samar da kaya (Cost of Sales) ya ƙaru zuwa Naira biliyan 902.24 daga Naira biliyan 764.52. Haka kuma, kuɗaɗen tallace-tallace, rabon kaya da gudanarwa sun tashi da kashi 43 cikin ɗari zuwa Naira biliyan 364.14.

Sakataren Kamfanin, Uaboi Agbebaku, ya danganta wannan ci gaba da “ci gaba da ƙirƙire-ƙirƙire, mayar da hankali kan kayayyakin manyan mataki (premiumisation), daidaitaccen farashi, da kuma ƙwarewar gudanar da kasuwanci.” Ya ƙara da cewa ribar aiki (operating profit) ta nuna tsauraran matakan rage kashe kuɗi, haɓaka yawan aiki, da inganta tsarin samar da kaya.

Ribar aiki ta ƙaru da sama da kashi 190 cikin ɗari, yayin da ribar net ta farfaɗo da kashi 168 cikin ɗari daga matsayin asara da kamfanin ya samu a 2023.

Wannan sauyi ya samu ne sakamakon raguwar kuɗin biyan bashin kuɗi (net finance costs) da kashi 83 cikin ɗari bayan shirin sayar da hannun jari ga masu ruwa da tsaki (Rights Issue) da kamfanin ya yi a 2023, wanda ya rage nauyin bashi da kuma tasirin canjin kuɗaɗen waje.

Duk da sakamakon mai ƙarfi, ajiyar ribar kamfanin (retained earnings) har yanzu tana a matsayin mara kyau saboda asarar da aka tafka a shekaru biyu da suka gabata. Sai dai hukumar gudanarwa ta ce farfaɗowar na tafiya daidai da yadda aka tsara.

A shekarar 2024 kuma, kamfanin ya kammala cikakken saye da haɗa kamfanin Distell Wines and Spirits Nigeria Limited, inda aka biya wasu kuɗaɗe na musamman na haɗa kamfanonin.

Matakin ya faɗaɗa kayayyakin kamfanin fiye da giya kawai, tare da ƙarfafa damar samun ci gaba na dogon lokaci.
Agbebaku ya tabbatar wa masu ruwa da tsaki cewa da goyon bayan masu hannun jari, ƙwarewa, ƙirƙire-ƙirƙire, da kuma tsare-tsaren kula da kuɗi cikin hikima, Nigerian Breweries na da kyakkyawan matsayi domin ci gaba da bunƙasa kasuwanci da samar da ƙima na dogon lokaci.