Trends

NNPP Ta Nesanta Kanta Daga Shirin Kwankwaso Na Komawa APC

Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta nesanta kanta daga labarin shirin tsohon ɗan takarar shugabancin ƙasa a 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, na komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Sakataren Ƙasa na NNPP, Dakta Ogini Olaposi, cikin wata sanarwa a ranar Litinin, ya bayyana cewa ikirarin da Kwankwaso ya yi na komawa APC abu ne na kansa tare da ƙungiyar Kwankwasiyya, kuma ba shi da alaka da NNPP.

Kwankwaso, wanda ya taba zama gwamnan Jihar Kano, ya sanar da cewa shi da magoya bayansa suna shirin shiga APC a ranar Asabar, sai dai ya yi gargadin cewa ƙungiyarsa ba za ta yarda a yi amfani da ita a watsar ba.

Amma a martaninsa, Olaposi ya ce wannan sanarwa hujja ce cewa Kwankwaso da mabiyansa ba su da alaƙa da NNPP, tunda an riga an kori su daga jam’iyyar saboda ayyukan cin amanar jam’iyya.

“Daga ƙarshe an tabbatar da gaskiyar mu. Dukkan tattaunawa da Kwankwaso daga yanzu za a yi su ne a matsayin nasa na mutum ɗaya,” in ji Olaposi.

Ya ƙara da cewa yarjejeniyar haɗin gwiwa tsakanin Kwankwasiyya da NNPP ta ƙare tun bayan zaɓen 2023. A cewarsa, rikicin jam’iyyar ya samo asali ne daga ƙoƙarin Kwankwaso da magoya bayansa na kwace tsarin jam’iyyar maimakon su fice cikin lumana.

Sakataren ya kuma bayyana cewa da dama daga cikin magoya bayan Kwankwaso a Kano sun riga sun koma APC, abin da ya bar shi ba tare da dandalin siyasa mai ƙarfi ba.

“Kwankwaso ba shi da jam’iyyar siyasa. Ƙimar siyasar sa ta faɗi bayan ya yaudari NNPP wacce ta ba shi kyauta dandali domin burin takarar shugaban ƙasa,” in ji Olaposi.

Ya jaddada cewa duk wata tattaunawa da aka yi a sunan Kwankwaso ba za ta taɓa da alaƙa da NNPP ba, tunda shi da ƙungiyarsa sun riga sun kasance a kore.

Olaposi ya kuma soki Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) kan jinkirin amincewa da sabon shugabancin jam’iyyar ƙarƙashin Dakta Agbo Major, wanda aka tabbatar da shi ta hanyar babban taron jam’iyya da kotu ta umurce shi.