Najeriya ta shigo da kusan lita biliyan 1.31 na man fetur a watan Disambar 2025, kamar yadda bayanai daga Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Tsakiyar da Ƙarshen Tsari (NMDPRA) suka nuna.
A daidai wannan lokaci, matatar man Dangote ta samar da lita miliyan 992, abin da ya nuna ƙaruwa mai yawa daga samarwar cikin gida idan aka kwatanta da watan Nuwamba. A Disamba, jimillar samar da man fetur ta kai lita miliyan 74.2 a rana, inda shigo da mai ya kai lita miliyan 42.2 a rana, yayin da Dangote ta samar da lita miliyan 32 a rana.
Wadannan alkaluma sun bambanta da na watan Nuwamba, lokacin da aka shigo da lita biliyan 1.57 na fetur, yayin da Dangote ta samar da lita miliyan 585 kacal. Matsakaicin samarwa a Nuwamba ya kai lita miliyan 71.5 a rana; an shigo da lita miliyan 52.1, yayin da lita miliyan 19.5 suka fito daga matatar Dangote, wacce ita ce kaɗai ke samar da fetur a Najeriya a lokacin rahoton.
An lura cewa ƙarin samar da man fetur daga lita biliyan 2.15 a Nuwamba zuwa lita biliyan 2.3 a Disamba ya nuna matsin buƙatar mai na lokacin bukukuwan Kirsimeti.
Haka kuma, an lura cewa duk da ci gaban tace mai a cikin gida, wasu ‘yan kasuwa na ci gaba da fifita shigo da fetur daga ƙasashen waje.
A wani rahoto da NMDPRA ta fitar kan watan Nuwamba, hukumar ta kare bayar da lasisin shigo da mai, tana mai cewa an samu ƙarancin mai a watan Satumba da Oktoba. Bayanai daga hukumar sun nuna cewa NNPC da sauran ‘yan kasuwa sun shigo da lita biliyan 1.5 na fetur a Nuwamba kaɗai.
Adadin shigo da lita miliyan 52.1 a rana a watan Nuwamba shi ne mafi girma tun bayan da matatar Dangote ta fara samar da fetur a watan Satumba 2024.
NMDPRA ta bayyana cewa ƙarancin samarwa a Satumba da Oktoba 2025, wanda ya kasa biyan buƙatar ƙasa, ya tilasta ƙara shigo da mai. Ta ce a watan Satumba, Dangote ta samar da lita miliyan 17.6 a rana, yayin da shigo da mai ya kai lita miliyan 22.1 a rana.
Da yake martani, Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya zargi tsohon Shugaban Hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed, da bayar da abin da ya kira “lasisin shigo da mai ba tare da tunani ba” alhali tankunan Dangote cike suke, yana mai zargin sa da yin zagon ƙasa ga tattalin arzikin ƙasa.
“Yanzu haka ma, tankunanmu cike suke saboda NMDPRA ta bayar da lasisi ba tare da hankali ba. Sai muka je muka kai ƙorafi ga gwamnati,” in ji Dangote.
Ya ƙara da cewa, “Yanzu suna shirin bayar da lasisi na kusan lita biliyan 7.5 don zangon farko na shekarar 2026, duk da cewa mun tabbatar da cewa za mu iya samar da isasshen adadi.”
Dangote ya kuma tayar da kasuwa ta hanyar rage farashin famfon fetur daga kusan N900 zuwa N739 kowace lita, duk da cewa hakan ya janyo asara mai yawa ga masu tace mai da masu shigo da shi.
A ranar Laraba, Daraktan Gudanarwa na matatar Dangote, David Bird, ya bayyana cewa matatar ta fara loda fetur da dare, yayin da take ƙara ƙoƙarin ci gaba da samar da fiye da lita miliyan 50 a rana a fadin Najeriya, lamarin da ke nuna cikakken sauya sheƙa zuwa aiki na awanni 24 a kowace rana a babbar matatar mai ta Afirka.
Da yake magana a wani taron manema labarai a matatar, Bird ya ce sauyawa zuwa lodin dare ya zama dole domin biyan buƙatar kasuwa da kuma inganta saurin fitar da kayayyaki.
A cewarsa, matatar yanzu tana biyan buƙatar lita miliyan 50 na fetur a rana a fannin samarwa da kuma fitarwa.
“Abin da nake matuƙar alfahari da shi shi ne, a rabin na biyu na shekarar 2025, duk da cewa muna ƙara ƙarfin ayyukanmu, mun sami damar samar da lita miliyan 50 a rana, har ma fiye da lita miliyan 52 a wasu lokuta,” in ji Bird.
Ya ƙara da cewa, “Mun riga mun fara lodin dare, don haka aiki ne na awanni 24. Mun kuma yi bikin fitar da fiye da lita miliyan 50, wanda ke nufin sama da manyan motoci dubu ɗaya na ratsa ƙofa da matattarar lodinmu a kowace rana.”
