Yayin da yawan hako danyen mai a Najeriya ya karu zuwa kusan ganga miliyan 1.8 a rana, kungiyoyin masu matatun mai da kungiyoyin kwadago sun sake kira da a kara samar da danyen mai ga matatun cikin gida tare da rage farashin fetur.
Mai magana da yawun Crude Oil Refiners Association of Nigeria (CORAN), Eche Idoko, ya bayyana cewa masu matatun mai za su kara matsa lamba domin samun karin danyen mai.
Ya ce duk da shirin Nigerian National Petroleum Company Limited na kara jigilar danyen mai zuwa Dangote Refinery daga lodin jiragen ruwa biyar zuwa bakwai a rana, hakan har yanzu bai kai bukatar lodin guda 14 da ake bukata ba.
Idoko ya jaddada cewa aiwatar da tsarin samar da danyen mai ga matatun cikin gida (Domestic Crude Supply Obligation – DCSO) na da matukar muhimmanci, amma matsalolin farashi sun hana matatun damar karbar danyen mai yadda ya kamata.
Ya ce, “Bakwai cikin 14 har yanzu nesa yake da abin da ake da shi.”
Ya kara da cewa samar da danyen mai ba tare da katsewa ba zai taimaka wajen kara ribar matatun mai da kudaden shiga na gwamnati, amma kananan matatun mai ba za su iya samun riba ba sai an daidaita farashin.
“Idan masu hakar mai suka ba mu danyen mai, za mu samu riba. Hakan yana nuna yadda harkar tace mai ke da anfani,” in ji shi.
Hukumar Nigerian Upstream Petroleum Regulatory Commission (NUPRC) ta tabbatar da karuwar yawan hako mai, inda ta ce ya tashi daga ganga miliyan 1.48 a watan Fabrairu zuwa miliyan 1.84 a watan Maris, tare da fatan kaiwa miliyan 2 a rana nan gaba.
Ministan Kudi, Wale Edun, ya yabawa wannan ci gaba, yana mai cewa “labari ne mai dadi kwarai” wanda ya dace da manufofin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.
A gefe guda kuma, Nigeria Labour Congress (NLC) ta ce wannan karin yawan hako mai ya kamata ya haifar da karin danyen mai ga matatun cikin gida da kuma rage farashin fetur a kasuwa.
Wani babban jami’in kungiyar ya yi gargadin cewa rashin cimma hakan zai nuna gazawa a tafiyar da tattalin arziki.
Kungiyar kwadagon ta kuma nuna damuwa kan rashin gaskiya, tana mai cewa ba a cika auna danyen mai yadda ya kamata a wuraren fitar da shi waje ba, wanda ke sa wuya a tabbatar da ainihin yawan da ake hakowa.
“Ba mu da tabbacin adadin danyen mai da ake hakowa kullum,” in ji jami’in.
NLC ta kara da cewa da yake farashin mai a kasuwar duniya ya haura dala 100 kan kowace ganga—fiye da dala 64 da aka sanya a kasafin kudin kasa—ya kamata Najeriya ta amfana da karin kudaden shiga.
Sai dai kungiyar ta yi gargadin cewa muddin karin yawan hako mai bai haifar da ingantacciyar kulawa, bunkasa matatun mai, da rage farashin ga al’umma ba, to jama’a ba za su ji wani anfani mai kyau ba.
