Trends

Manoman Najeriya Sun Yi Asarar N5trn Cikin Shekaru Biyu – Rahoto

Manoman Najeriya sun yi asarar kusan Naira tiriliyan 5 (N5trn) na jarin samarwa a cikin shekaru biyu da suka gabata, a cewar wani sabon rahoto da Gidauniyar Kwararru Kan Zaman Lafiya (Foundation for Peace Professionals – PeacePro) ta fitar.

Ƙungiyar ta ce asarar ta samo asali ne daga faɗuwar farashi sakamakon manufofin gwamnati, hasashen yanayi marasa inganci daga Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMet), da kuma rikicewar kasuwanni mai tsanani.

“Sashen noma na ƙasar na nutsewa cikin babbar matsalar tsari,” in ji PeacePro a cikin sanarwarta, tana mai gargaɗin cewa halin da ake ciki ya riga ya rushe tubalin samar da abinci.

Daraktan Zartarwa na PeacePro, Abdulrazaq Hamzat, ya bayyana asarar a matsayin lalacewar jarin noma kai tsaye a matakin masu samarwa.

Ya jaddada cewa wannan ƙididdigar ba ta haɗa da tasirin tattalin arziƙi na gaba ba, kamar hauhawar farashin kaya ga masu saye, raguwar GDP, matsin lambar canjin kuɗin waje, ko kuma kuɗaɗen da suka shafi tsaro.

“Waɗannan tasirin za su zo daga baya. Abin da ya riga ya faru shi ne rushewar jarin manoma,” in ji Hamzat.

Rahoton ya nuna cewa tsakanin 2024 zuwa 2025, manoma sun rasa ikon sarrafa farashin abinci sakamakon manufofin da aka aiwatar ba a kan lokaci ba, hanyoyin danne farashi, raunin daidaiton kasuwa, da kuma hasashen yanayi da ba a iya dogaro da su.

Waɗannan abubuwa sun tilasta wa masu noma sayar da amfanin gona ƙasa da kuɗin da suka kashe, lamarin da ya shafe jarin da ake buƙata domin ci gaba da zagayen samarwa na gaba. “Wannan ba gyaran kasuwa ba ne. Girgizar manufofi ce da ta kwashe daraja daga hannun masu samarwa,” in ji sanarwar.

Duk da cewa ana kiyasta cewa mutane miliyan 38 zuwa 40 ne ke shiga harkar noma a Najeriya, PeacePro ta jaddada cewa mummunar asarar ta fi shafar manoman da ke hulɗa da kasuwa, ba manoman ciyar da kai kawai ba.

“Mafi shafar sune manoma miliyan 6 zuwa 8, ciki har da ƙanana da matsakaitan manoman kasuwanci, manoman da ba su da isasshen wurin ajiya kuma ke karɓar farashin kasuwa yadda aka kayyade, da kuma waɗanda ke noma hatsi, dankali/tubers, kayan lambu da wake-wake (legumes),” in ji ƙungiyar.

PeacePro ta kwatanta girman wannan lalacewa da rugujewar sashen kuɗi, tana mai nuna wani muhimmin bambanci. “Wannan rikici bai faru a bankuna ko kasuwannin hannun jari ba. Ya faru ne a ɓoye, a gonaki da ƙauyuka,” in ji sanarwar.

Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa raguwar jarin manoma zai kai ga raguwa a noman 2026, ƙarancin samar da abinci a cikin gida, ƙarin hauhawar farashin abinci, ƙaruwa talauci a karkara, da kuma tashin hankali a zamantakewa.

“Najeriya za ta biya farashin manufofin da suka ɗauki manoma a matsayin matattarar shan girgizar hauhawar farashi, muddin ba a gyara lamarin a kan lokaci ba,” in ji PeacePro.