Najeriya na dab da zama ƙasar Afirka ta farko da za ta kera motocin lantarki (Electric Vehicles – EVs) bayan ta kulla yarjejeniyar haɗin gwiwa da Kwamitin Raya Tattalin Arziƙin Asiya na Koriya ta Kudu (Asia Economic Development Committee – AEDC).
Gwamnatin Tarayya ta sanya hannu kan Yarjejeniyar Fahimta (MOU) da AEDC a ranar 30 ga Janairu, 2026.
Karamin Ministan Masana’antu, Sanata John Enoh, ne ya sanya hannu a madadin Gwamnatin Tarayya, yayin da Shugaban AEDC, Mista Yoon Suk-hun, ya sanya hannu a madadin ƙungiyar Koriya ta Kudu.
Wannan haɗin gwiwa ya yi daidai da Tsarin Sauyin Makamashi na Ƙasa (National Energy Transition Plan – ETP) da kuma Tsarin Bunƙasa Masana’antar Motoci na Ƙasa (National Automotive Industry Development Plan – NAIDP) na Najeriya.
A cewar bayanan da aka fitar, za a aiwatar da aikin ne a matakai, inda za a fara da haɗa motocin lantarki (EV assembly) kafin a faɗaɗa zuwa cikakken kera motoci a cikin gida.
An kiyasta cewa masana’antar za ta samar da motoci kusan 300,000, tare da ƙirƙirar ayyukan yi kimanin 10,000 ga ’yan Najeriya.
Hukumar National Automotive Design and Development Council (NADDC) ta bayyana cewa, “Za a aiwatar da aikin ne a matakai, farawa da haɗa motocin lantarki sannan a faɗaɗa zuwa cikakken kera su a cikin gida, tare da ƙarfin samar da motoci 300,000 da kuma samar da ayyukan yi kusan 10,000.”
Daraktan Janar na NADDC, Otunba Oluwemimo Joseph Osanipin, ya sake jaddada cewa shirin na da babbar dama wajen bunƙasa ci gaba mai ɗorewa a sashen masana’antar motoci a Najeriya.
Ya nuna muhimmancin canja fasaha (technology transfer) da kuma bincike, ƙira da ƙirƙire-ƙirƙire (research, design and innovation).
A cewarsa, “Wannan shiri zai hanzarta canja fasaha, jawo zuba jari, bunƙasa jarin ɗan Adam, da kuma ƙarfafa bincike, ƙira da sabbin ƙirƙire-ƙirƙire.”
NADDC ta ƙara da cewa Najeriya na ci gaba da gina tsayayyen tsarin masana’antar motoci da ke tallafa wa kera kayayyaki a cikin gida, amfani da makamashi mai tsafta, da kuma gasa a kasuwar duniya. An bayyana wannan haɗin gwiwa a matsayin babban mataki na cimma waɗannan manufofi.
Ana sa ran aikin zai yi tasiri mai kyau ga tattalin arziƙin Najeriya, ta hanyar samar da sabbin damammaki ga kasuwanci da daidaikun mutane. Haka kuma, yarjejeniyar ta ƙunshi gina muhimman cibiyoyin cajin lantarki (charging infrastructure) a faɗin ƙasar domin tallafa wa amfani da motocin lantarki.
