Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da aiwatar da babban sauyi a fannin ilimi da zai bai wa Kwalejojin Ilimi a faɗin ƙasar damar gudanar da shirin takardar shaidar NCE da kuma shirin digiri kai tsaye ba tare da haɗin gwiwar jami’a ba.
Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, wanda Ministan Jiha na Ilimi, Suwaiba Said Ahmad ta wakilta, ya bayyana hakan a taron kolin kasa da aka gudanar a Abuja a ranar Talata. Ta ce wannan mataki wani “babban tarihi ne a ci gaban ilimin Najeriya.”
“Da farko a tarihinmu, kwalejojin ilimi sun samu doka da izinin gudanar da NCE da shirye-shiryen digiri a lokaci guda a fannoni na koyar da malamai,” in ji ta, tana nuni da Dokar Kafa Kwalejojin Ilimi ta Tarayya, Lamba 43 ta 2023.
Ministan ta bayyana cewa sauyin ya ginu ne a kan kwarewa da gogewa da wadannan cibiyoyi suka nuna tsawon shekaru.
“Tsalakar tsarin doka yanzu ya ba su ikon faɗaɗa shirin karatu tare da ci gaba da babbar manufarsu ta samar da malamai ƙwararru da nagartattu,” ta ƙara da cewa.
Shugaban Hukumar Kula da Kwalejojin Ilimi ta Ƙasa (NCCE), Farfesa Paulinus Chijioke Okwelle, ya bayyana wannan sauyi a matsayin “na tarihi,” yana mai cewa zai farfaɗo da ilimin koyarwa tare da faɗaɗa damar shiga ga ɗalibai masu neman zama malamai.
“Tsawon shekaru, kwalejojin ilimi suna haɗa kai da jami’o’i don ba da digiri. Yau, da cikakken izinin doka, sun samu ’yancin gudanar da shi kai tsaye ta amfani da ƙarfin ma’aikata, gine-gine da ƙwarewar ilimi da suke da shi,” in ji shi.
Ya jaddada amfanin tsarin biyu, ciki har da samar da ɗalibai da ke da shaidar NCE da digiri (B.Ed), samar da malamai ƙwararru a kai a kai, da kuma riƙe ƙwararrun malamai a cikin tsarin.
Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Kwalejojin Ilimi na Tarayya, Hon. Adamu Tanko, ya tabbatar wa masu ruwa da tsaki cewa “darajar digirin da kwalejojin ilimi za su bayar ta yi daidai da wacce ake bayarwa a jami’o’i na gargajiya a ƙasar.”
Ma’aikatar Ilimi ta kuma yi alkawarin ci gaba da bayar da goyon baya ta hanyar manufofi, taimakon fasaha da samar da albarkatu domin tabbatar da nasarar aiwatar da wannan sabon tsari.
A da, Kwalejojin Ilimi a Najeriya suna da iyaka ne kawai wajen bayar da takardar shaidar NCE, kuma sai da haɗin gwiwar jami’o’i ake gudanar da shirye-shiryen digiri.
