Kudirin Kasafin Kuɗin 2026 ya ware Naira tiriliyan 1.38 domin biyan fansho, garatuti da sauran haƙƙoƙin tsofaffin ma’aikata a fadin hukumomin Gwamnatin Tarayya, hukumomin tsaro, hukumomin gwamnati (parastatals) da jami’o’i.
A ƙarƙashin wannan rabon kuɗi, Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya zai karɓi Naira biliyan 94.54 domin fanshon ma’aikatan farar hula, ciki har da garatuti, kuɗin tafiyar da harkokin fansho da biyan basussukan da ba a tanada kuɗinsu ba. Fanshon ma’aikatan farar hula kaɗai ya kai Naira biliyan 60.34, yayin da bashin ƙarin fansho na shekarar 2024 ya kai Naira biliyan 30.58.
An ware Naira biliyan 486.04 domin fansho da garatuti na sojoji, wanda ya haɗa da kuɗin da aka tanada ga waɗanda ake sa ran za su yi ritaya (N130.38bn), biyan fansho da garatuti (N237.25bn), haƙƙoƙin mutuwa (death benefits) na Naira biliyan 98.53, da kuma kuɗaɗen gudanarwa. Haka kuma, an tanadi kuɗi na musamman ga sojojin da suka yi ritaya saboda rashin lafiya da kuma bashin fansho daga Janairu 2019 zuwa Disamba 2021.
Hukumomin tsaro ma sun amfana da wannan kasafi, inda Hukumar Tsaron Farar Hula (DSS) ta samu Naira biliyan 28.61, Hukumar Leken Asiri ta Ƙasa (NIA) ta samu Naira biliyan 23.54, yayin da fanshon ‘yan sanda ya kai Naira biliyan 18.53. Ofishin Fansho na Kwastam, Shige da Fice da Gidajen Gyaran Hali (Prisons) zai karɓi Naira biliyan 18.41.
Hukumomin gwamnati da jami’o’i za su raba Naira biliyan 207.81, yayin da Hukumar Kula da Fansho ta Ƙasa (PenCom) ta samu Naira biliyan 427.04 domin garatuti, kariyar fansho da gyare-gyaren da suka biyo bayan sauye-sauyen albashi. Sauran tanade-tanaden sun haɗa da haƙƙoƙin tsofaffin shugabannin ma’aikata, farfesoshi da suka yi ritaya, tsofaffin ma’aikatan EFCC, da inshorar rai ta ƙungiya (group life assurance) ga dukkan ma’aikatun gwamnati (MDAs), wanda ya kai jimillar Naira tiriliyan 2.19 a ƙarƙashin tanadin kuɗin gama-gari na gwamnati (service-wide votes).
Tanadin kuɗaɗen fansho na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka ƙunshi kasafin 2026, abin da ke nuna ƙudurin Gwamnatin Tarayya na cika alkawuran da take da su ga tsofaffin ma’aikata tare da daidaita bashin da aka tara da kuma waɗanda ba a tanada kuɗinsu ba.
