Kamfanonin rarraba wutar lantarki a Najeriya (DisCos) sun yi watsi da sabon umarnin Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) wanda ya wajabta musu buɗe asusun musamman na kashe kuɗaɗen ayyukan inganta kayayyakin more rayuwa (CapEx), suna mai cewa hakan tsoma baki ne a harkokin gudanar da kamfanoni masu zaman kansu.
Umarnin, wanda ke ƙunshe cikin Order No. NERC/2026/062, ya fara aiki daga ranar 1 ga Yulin 2026, kuma ya tanadi cewa bayan kamfanonin sun biya dukkan basussukan kasuwar wutar lantarki da kuɗaɗen gudanarwa, dole ne su tura wani babban kaso na kuɗaɗen da suka rage zuwa asusun CapEx.
A ƙarƙashin sabon tsarin, kamfanonin da ba su da bashi za su tura kashi 70 cikin ɗari na kuɗaɗen da suka rage zuwa asusun CapEx, yayin da za su riƙe kashi 30 cikin ɗari kacal domin gudanar da harkokinsu.
Ga kamfanonin da ke da bashi kuwa, za su biya kashi 25 cikin ɗari ga Kamfanin Sayen Wutar Lantarki na Najeriya (NBET), kashi 25 cikin ɗari ga Mai Gudanar da Kasuwa (Market Operator), kashi 35 cikin ɗari zuwa asusun CapEx, sannan su riƙe kashi 15 cikin ɗari kawai.
Wani daga cikin kamfanonin ya ce wannan umarni na nuna cewa NERC na ƙoƙarin mallake yadda DisCos ke kashe kuɗaɗensu, yana mai cewa ko kamfanin da ba shi da bashi zai riƙe kashi 30 cikin ɗari ne kawai na abin da ya rage.
Sabon tsarin ya kuma tanadi cewa kuɗaɗen da ke cikin asusun CapEx za a iya amfani da su ne kawai wajen aiwatar da ayyukan Performance Improvement Plan (PIP) da NERC ta amince da su, tare da buƙatar samun amincewar hukumar a matakai daban-daban kafin a kashe kuɗin.
Kamfanonin sun ce hakan na nufin NERC na ɗaukar matsayin kwamitocin gudanarwa na kamfanonin.
Wani jami’in kamfani ya yi gargaɗin cewa wannan mataki na iya razanar da masu zuba jari tare da buɗe ƙofa ga cin hanci wajen bayar da kwangiloli, yana mai cewa tsarin ya fi kama da ƙoƙarin ƙwace iko.
Sai dai NERC ta kare matakin, tana mai cewa binciken da ta gudanar kan kuɗaɗen shiga na shekarar 2025 ya nuna cewa wasu DisCos sun samu isassun kuɗaɗen da za su iya gudanar da ayyukansu, amma ba su saka kuɗi yadda ya kamata wajen inganta cibiyoyin rarraba wutar lantarki ba.
Hukumar ta ce sabon umarnin ya zama dole domin tabbatar da cewa ana amfani da kuɗaɗen wajen gyara, faɗaɗa da kuma inganta hanyoyin rarraba wutar lantarki, kamar yadda Dokar Wutar Lantarki ta 2023 ta tanada.
Sai dai wasu masu ruwa da tsaki sun yi gargaɗin cewa kulle kashi 70 zuwa 85 cikin ɗari na kuɗaɗen shiga na iya rage wa kamfanonin damar gudanar da ayyukansu cikin gaggawa, hana samun kuɗaɗen tallafi daga masu zuba jari, tare da haifar da matsalolin shari’a saboda ba a tuntubi kamfanonin kafin fitar da umarnin ba.
