Trends

Juyin Mulki: Sojoji Sun yi wa Jonathan Rakiya Yayin Ficewa Daga Guinea-Bissau

Goodluck Jonathan tsohon Shugaban kasan Nigeriya yayin fitar shi daga Guinea Bissau

Tsohon Shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan ya samu rakiyar jami’an sojoji a lokacin da yake ficewa daga cikin ƙasar Guinea-Bissau, a yayin da ake cigaba da zaman ɗar-ɗar bayan sojoji sun karɓe mulkin ƙasar.

Da fari an ruwaito cewa Jonathan yana ɗaya daga cikin jagororin Afirka da juyin mulkin ƙasar ya rutsa da su.

An zaɓi tsohon shugaban ne domin ya shiga sahun mutane 36 masu sanya ido a zaɓen shugaban ƙasa a Guinea-Bissau ƙarƙashin haɗakar AU, ECOWAS da WAEF.

Saidai, zuwa jiya Laraba rundunar sojoji ta sanar da karɓe iko da mulkin ƙasar bayan manyan ƴan takara biyu ciki har da Shugaba Umaro Sissoco Embalo suka yi ikirarin nasarar lashe zaɓen, wanda aka gudanar a ranar Lahadi.

A cewar ShaharaReporters, tuni Jonathan, wanda ya kasance ciki matsi, ya samu rakiya zuwa wajen ƙasar, inda kuma ake sa ran zai dawo Nijeriya a yau.