Trends

Shugaba Tinubu ya Ayyana Dokar ta Baci Kan Tsaron kasa

Bola Ahmed Tinubu Shugaban Kasar Nigeriya

Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Laraba ya ayyana dokar ta-baci kan harkokin tsaro a fadin kasar, inda ya umarci Rundunar ‘Yan Sanda da Sojoji su kara daukar ma’aikata domin karfafa yaki da karuwar matsalar tsaro a fadin Najeriya.

A wata sanarwa da ta fito daga fadar shugaban kasa, shugaban ya umurci ‘yan sanda su dauki karin jami’ai 20,000, wanda hakan zai kai adadin wadanda ake shirin dauka zuwa 50,000.

Haka kuma ya amince da amfani da sansanonin NYSC a matsayin wucin-gadi wajen horas da sababbin jami’an.

Sanarwar ta ce, “A yau, ganin halin tsaro da ake ciki, na yanke shawarar ayyana dokar ta-baci kan tsaro a fadin kasa tare da bayar da umarnin karin daukar ma’aikata cikin rundunonin tsaro.

“Daga wannan sanarwa, an bai wa ‘yan sanda da sojoji izinin kara daukar jami’ai. ‘Yan sanda za su kara daukar jami’ai 20,000, wanda zai kai adadin zuwa 50,000.

“Kodayake tun da farko na amince da inganta cibiyoyin horar da ‘yan sanda a fadin kasa, daga wannan sanarwa, hukumomin ‘yan sanda na da izinin amfani da sansanonin National Youth Service Corps a matsayin wuraren horo.

“Jami’an da za a cire daga tsare-tsaren VIP za a tura su horo na gaggawa domin sake horas da su tare da bunkasa ingancin ayyukan tsaro da za su bayar idan an tura su yankunan da ke fama da matsalar tsaro a kasar.