Jihohi goma sha biyar a Najeriya sun ware jimillar Naira tiriliyan 10.7 domin kashe kuɗaɗen ci gaba (capital expenditure) a kasafin kuɗin shekarar 2026, inda aka fi mai da hankali kan gina hanyoyi, makarantu, asibitoci da sauran muhimman ayyukan jama’a. Daga cikin jihohin da abin ya shafa akwai Lagos, Akwa Ibom, Enugu da Imo.
Jihar Ebonyi ce ke kan gaba wajen ware kuɗaɗen ci gaba, inda ta tanadi Naira biliyan 749.49, wanda ya kai kashi 84.7 cikin 100 na kasafin kuɗinta. Sai kuma Jihar Imo da ta ware Naira tiriliyan 1.2 (kashi 83.4 cikin 100), da Jihar Enugu da ta tanadi Naira tiriliyan 1.29 (kashi 80 cikin 100).
An bayyana cewa kuɗaɗen da aka tanada za su fito ne daga hanyoyi daban-daban da suka haɗa da lamuni, takardun bashi (bonds), tallafi (grants) da kuma haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu (PPP). Masana tattalin arziki sun shawarci gwamnonin jihohi da su ƙara ƙarfafa hanyoyin samun kuɗaɗen cikin gida tare da jawo hankalin masu zuba jari.
Jihar Lagos, wadda ke da mafi girman kasafin kuɗi na Naira tiriliyan 4.237, ta ware kashi 29.2 cikin 100 ne kacal don ayyukan ci gaba. Sauran jihohi sun fi ba da fifiko ga gine-ginen more rayuwa, ciki har da Kaduna (kashi 70.9), Edo (kashi 67.8) da Kano (kashi 63.3).
Haka kuma, Jihar Yobe ta ware Naira biliyan 291.9 (kashi 56.6), Oyo ta tanadi Naira biliyan 505 (kashi 56.6), yayin da Osun ta ware Naira biliyan 388.38 (kashi 55). Jihar Ondo ta tanadi Naira biliyan 303.58, wanda ya kai kashi 57.9 cikin 100 na kasafin kuɗinta.
Masana sun jaddada cewa dorewar kuɗaɗen jihohi na buƙatar tattalin arzikin cikin gida mai ƙarfi, faɗaɗa tushen haraji, da kuma hikimar haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu. A cewar Dr. Ayodeji Ebo, “jawo hankalin masu zuba jari na buƙatar ingantattun hanyoyin more rayuwa da manufofi masu tabbas da kwanciyar hankali.”
