Trends

ICAN: Ana Zargin Wata Mata daRubuta Jarabawa Wa Kwamishiniyar Kuɗi naTaraba

An cafke wata mata tana zargin rubuta jarabawar Institute of Chartered Accountants of Nigeria (ICAN) da sunan Kwamishiniyar Kuɗi a Jihar Taraba, Sarah Enoch Adi.

A wani bidiyo da Sahara Reporters ta wallafa, jami’an kula da jarabawa sun tsayar da wacce ake zargi, wadda ta bayyana kanta da suna Leavitt Felix. Amma takardun rijista sun nuna cewa ainihin mai rijistar jarabawar ita ce kwamishiniya Sarah Enoch Adi.

Lokacin da aka matsa mata, Felix ta amince cewa tana rubuta jarabawar ne da sunan Sarah Adi. Amma da aka tambaye ta sunanta, ta ce: “Ni dai sunana Leavitt Felix.”

Jami’an kula da jarabawar sun lura da rashin daidaito tsakanin bayanan da ta bayar da kuma bayanan da ke cikin rijista. Daya daga cikin jami’an ya tunatar da ita cewa a baya ta ce tana aiki a ma’aikatar kuɗi, wanda ke da alaƙa da mukamin kwamishiniyar.

Kodayake Felix ta amince cewa tana rubuta jarabawar ne da sunan wani, ta ce ba ta san Sarah kai tsaye ba. Ta bayyana cewa wani mutum mai suna Joshua ne ya ɗauke ta aiki, amma ta ce ba ta san sunan mahaifinsa ko inda yake aiki ba.

Jami’an jarabawar suka gargade ta cewa za su kai lamarin ga ‘yan sanda idan ta ƙi bayar da ƙarin bayani. “Dukkan bayanan da muke samu a nan… za mu tabbatar da su ta hanyar ‘yan sanda,” in ji jami’in. “Muna so mu sauƙaƙa maka. Idan kika bayar da gaskiya, za ki tafi. Babu buƙatar bata lokaci.”

Wannan na zuwa ne bayan wasu sabani da dama da suka shafi kwamishiniyar tun bayan nada ta. A watan Agusta, ma’aikatan gwamnati a Taraba sun bukaci Gwamna Agbu Kefas da ya tsige Akanta Janar na Jihar, Mista Gauis Danjuma, da Kwamishiniyar Kuɗi, Sarah Adi, saboda zargin rashin gaskiya a binciken tantancewar ma’aikata ta hanyar biometric.

Ma’aikatan da suka shiga yajin aiki sun koka cewa an cire sunayen sama da 7,000 daga cikin ma’aikata, ciki har da na Daraktoci da Mataimakan Daraktoci daga albashi. Sun yi kira ga gwamnati ta nada sabbin masu iya aiki domin gyara kura-kuran.

A watan Yuni 2025, gwamnatin Taraba ta gudanar da binciken biometric ta Ofishin Akanta Janar tare da kulawar Kwamishiniyar Kuɗi, Sarah Adi, wanda ya kammala da bayyana sama da ma’aikata 7,000 a matsayin “ma’aikatan bogi.”

A cewar kungiyar Kwamishinonin Kuɗi na Najeriya, Sarah Adi ta haife ne a ranar 9 ga Afrilu, 1973, a Wukari, Jihar Taraba.

Ta kammala Digirin Doktora a fannin Accounting daga Jami’ar Jihar Nasarawa (NSUK) a 2023, da kuma Digiri na biyu a Banking and Finance daga Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) a 2011. Haka kuma ta yi HND (2006) da ND (2004) a fannin Accountancy daga Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Filato, Jos.

A watan Agusta 2023, Gwamna Agbu Kefas ya nada ta a matsayin Kwamishiniyar Kuɗi, Tsare-tsaren Kasafin Kuɗi da Tattalin Arziki na Jihar Taraba, mukamin da har yanzu take rike da shi.