Gwamnatin Tinubu Ya Gaza a Daidai Lokacin da Yan Fashin Daji Ke Karbar Haraji daga Manoma – ADC

Mallam Bolaji Abdullahi Mai Magana da Yawun Jam’iyyar ADC

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta bayyana rahoton karbar sama da Naira miliyan 56 daga manoma a Jihar Zamfara da kungiyoyin makamai suka yi a matsayin alamar gazawar gwamnati, tana mai kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki gaggawar matakan shawo kan lamarin.

Jam’iyyar ta kuma ce bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta na nuna “wani kauye baki daya a karamar hukumar Ifelodun ta Jihar Kwara da aka barshi ga ‘yan fashi” a karkashin shugabancin Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC ya nuna cewa Najeriya na shiga wani mummunan hali na gazawar gwamnati.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na kasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya sanya hannu, ADC ta bayyana cewa lamarin da manoma ke biyan kudade ga ‘yan ta’adda kafin su iya shiga gonakinsu ba matsalar Zamfara kadai ba ce, illa kuwa gargadi ne ga kasa baki daya.

“Idan jama’a za su yi watsi da gari baki daya saboda tsoron ‘yan fashi, musamman a tsakiyar kasar nan, wannan ba karamin al’amari ba ne — hujja ce ta mika wuya daga gwamnati,” in ji shi.

Abdullahi ya ce idan kungiyoyin makamai za su iya karbar Naira miliyan 56 daga manoma a matsayin “izini” na shuka amfanin gona, to batun ya wuce matsalar rashin tsaro yana nuna akwai miyagu da ke kalubalantar ikon mallakar wani bangare na Najeriya. Kuma idan masu laifi za su iya karbar haraji daga ‘yan kasa da bindiga, hakan na nufin gwamnati ta mika wuya wajen rike karfin iko.

Ya kuma nuna damuwarsa cewa irin wannan na faruwa a kasar da ke da daya daga cikin manyan kasafin kudin tsaro a Afirka, amma duk da haka ana barin manoma suna tattaunawa da shugabannin ‘yan fashi don su tsira. Ya tuna cewa a makon jiya a Zamfara, an sace mutane kusan 50 a lokaci guda.

Abdullahi ya kara bayyana cewa akwai hoton ban tsoro na gari baki daya inda matasa, tsofaffi, da marasa lafiya suka tsere saboda tsoron harin ‘yan fashi. Ya ce akwai wasu misalai da ke nuna wata barazana mai tayar da hankali da ka iya yaduwa zuwa sassan kasar da ake ganin suna cikin tsaro.

“Tambayar ita ce: shin gwamnatin Tinubu ta APC har yanzu na rike da iko ne kuma za a iya amincewa da ita wajen aiwatar da mafi muhimmancin aikinta kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya?” in ji shi.

Ya kuma tunatar da cewa a watan Nuwamba 2014, Tinubu, a lokacin da yake jagoran adawa, ya bukaci Shugaba Goodluck Jonathan ya yi murabus saboda matsalar Boko Haram a Arewa maso Gabas. A lokacin, Tinubu ya ce:

“Idan kana da ikon sarrafa rundunar soji, me yasa wani bangare na kasar zai kasance karkashin mamaya? A kowace kasa mai bin doka, shugaban ya kamata ya yi murabus.”

Abdullahi ya ce duk da cewa matsalar tsaro da Tinubu ya yi amfani da ita wajen yakin neman zabe a 2014 ta ninka a karkashin jam’iyyarsa, kuma yanzu ta yi muni a lokacin shugabancinsa, babu wanda ke kiransa da ya yi murabus.

“Ba ma bukatar Shugaba Tinubu ya yi murabus,” in ji shi, “muna bukatar ya yi aikinsa. Me ya sa zai ga ya dace a ayyana dokar ta baci a Jihar Rivers saboda tsaro, amma a Zamfara inda ake garkuwa da mutane da karbar haraji daga manoma ba ma samun ko jawabi kai tsaye daga gare shi?”

Ya kammala da cewa idan gwamnatin Tinubu ba za ta iya tabbatar da tsaron gonaki da al’ummomin karkara ba, idan mutane za su iya tserewa daga gidajensu saboda tsoro, to ta gaza wajen mafi muhimmancin aikinta.

“Ba za ka ce kana rike da iko a kasar ka ba yayin da ‘yan kasa ke tattaunawa da masu laifi don su tsira,” in ji Abdullahi.