Fitaccen dan Ƙasuwa Isyaku Ibrahim, Ya Rasu Yana da Shekaru 88

An rasa fitaccen ɗan kasuwa kuma dattijon siyasa, Alhaji Isyaku Ibrahim, wanda ya kasance abokin kusa da marigayi Shugaban Ƙasa Shehu Usman Shagari.

Ibrahim ya rasu ne da safiyar Asabar a wani asibiti mai zaman kansa da ke Abuja yana da shekaru 88.

An bayyana shi a matsayin gogaggen ɗan siyasa da ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa jam’iyyar da ta yi mulki a Jamhuriyar Tarayyar Najeriya ta Biyu, wato National Party of Nigeria (NPN). Asalinsa daga garin Mangar, yankin Farin Ruwa Area Administrative Council na karamar hukumar Wamba, jihar Nasarawa.

Shi ne wanda ya kafa kulob din kwallon kafa na Mighty Jets na Jos a shekarun 1970, kuma shi ne ɗan Najeriya na farko da ya ɗauko kocin ƙasashen waje daga Brazil don jagorantar kulob ɗin.

Ibrahim ya kuma sayi sabon babbar motar alfarma ga tawagar, ya kashe miliyoyin naira wajen tallafawa ƙungiyar Mighty Jets Football Club ta Jos har ta kai ga samun nasarori a lokacin da ta shahara sosai.

Haka kuma, yana daga cikin ’yan Najeriya na farko biyu da suka mallaki jirgin sama na haya.

Ɗan’uwansa, Dakta Musa Ibrahim, tsohon sakatare na dindindin, ya tabbatar da rasuwar dattijon ga jaridar Daily Trust.

Ya ce, “Da cikakken mika wuya ga hukuncin Allah, ina sanar da rasuwar ɗaya daga cikin manyan fitattun ’yan siyasar Najeriya kuma babban mai taimako ga al’umma, kawuna, Alhaji Isyaku Ibrahim. Ya rasu yau (Asabar). Za a yi sallar jana’izarsa bayan sallar Azahar a Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja.

“Ga waɗanda suka san shi, Alhaji mutum ne mai ƙa’idodi da kishin ƙasa, ɗaya daga cikin ’yan siyasar Arewa ’yan kaɗan da ke da ƙaunar yankin a zuciyarsu. Allah Ya jikansa, Ya ba shi Aljanna.”