Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya bayyana cewa majalisar na tare da shirin ɗaukar bashi na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa bashi kayan aiki ne da ba za a iya gujewa ba wajen bunƙasa tattalin arzikin Najeriya da kuma rage talauci.
Abbas ya bayyana haka ne a Abuja ranar Litinin, a taron shekara-shekara na 8 na African Network of Parliamentary Budget Offices (AN-PBO).
Ya karyata rahotannin da ke cewa majalisar na adawa da shirin ɗaukar bashi na gwamnatin Tinubu, yana kiran su da “yaudara da kuma ɓata-gari.”
“Kwanan nan, wani jawabi da shugaban marasa rinjaye ya gabatar a taron majalisun dokokin yammacin Afirka (WAPC) an fassara shi da gangan ta hanyar da ta sa mutane sun ɗauka cewa Majalisar Wakilai ba ta goyon bayan shirin ɗaukar bashi na gwamnatin Shugaba Tinubu. Muna so mu bayyana a fili cewa wannan fassara ba ta da tushe kuma yaudara ce,” in ji shi.
Abbas ya jaddada cewa Majalisar Wakilai ta 10 da kuma Majalisar Dokoki gaba ɗaya, sun sha nanata cewa, idan aka dubi bukatun ci gaban ƙasa, shirin ɗaukar bashi cikin tsari da hankali muhimmin kayan aiki ne na tattalin arziki.
“Kamar kowace ƙasa ta zamani, dole wani lokaci Najeriya ta yi amfani da bashi domin gina muhimman ayyuka, farfaɗo da ci gaba, da kuma kare al’umma masu rauni. Abin da ya fi muhimmanci kuma shugaban ƙasa ya tabbatar da shi shi ne, duk wani bashi da aka ɗauka za a yi shi cikin tsari, a bayyane, kuma a cikin tsarin dogon lokaci na kula da bashin Najeriya, bisa ga ƙa’idodin duniya,” in ji shi.
Kakakin ya ƙara da cewa ƙarƙashin shugabancin Tinubu, ana karkatar da kuɗaɗen bashi zuwa manyan ayyukan raya ƙasa da za su ƙara wa gwamnati kuɗin shiga, irin su wutar lantarki, sufuri da noma, maimakon a cinye su ba tare da amfani ba.
“Majalisa tana tsayawa daram wajen goyon bayan hangen nesa na Shugaba Tinubu na amfani da bashi cikin hikima domin haɓaka tattalin arziki da rage talauci, tare da ƙarfafa hanyoyin kulawa da sa ido,” Abbas ya jaddada.
Ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa shirin ɗaukar bashi na Tinubu yana gudana cikin tsari da hikima tare da bin ƙa’idodin duniya, kuma an karkatar da kuɗaɗen ne zuwa muhimman ayyuka masu sauya fasalin ƙasa.
Haka kuma, Abbas ya jawo hankali kan kafa National Assembly Budget and Research Office (NABRO) a matsayin muhimmin gyara da zai rika bayar da bincike mai zaman kansa kan batutuwan bashi, dorewar bashi, da manufofin kudi.
Ya kuma jaddada cewa duk da cewa bashi yana da muhimmanci, to, toshe ɓarakar da rashawa da kuma zubar da kuɗi ya fi muhimmanci. Ya ce Najeriya na asarar kusan dala biliyan 18 duk shekara ta hanyar harkokin kudaden haram, wanda ya kai kusan 3.8% na GDP.
Abbas ya nanata cewa bashi cikin tsari, haɗe da sa ido mai tsauri da kuma gyaran yaki da rashawa, shi ne zai kare makomar tattalin arzikin Najeriya.
