Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta dawo bakin aiki a majalisar dattawa bayan ofishinta ya sake budewa, bayan dakatarwar watanni shida da aka yi mata.
Sanatar ta isa harabar majalisar a ranar Talata, 23 ga Satumba, tare da magoya bayanta, sa’o’i bayan jami’an tsaro na majalisar (sergeant-at-arms) suka bude ofishinta.
“Lokacin da muke kotu, na karanta a cikin jaridu cewa an bude ofishinmu. Har ma na ga bidiyo da sakataren majalisar kansa yana bude kofar,” in ji Akpoti-Uduaghan ga ’yan jarida kafin ta shiga ofishinta.
Sai dai ta bayyana cewa ba a turo mata wata takardar hukuma ba kan dawo da ita bakin aiki.
“A halin yanzu, babu wata sanarwa ta hukuma da aka aiko mana. Ina tsammanin irin wannan babbar cibiya kamar Majalisar Dattawa za ta bi ka’idojin gudanarwa ta hanyar rubutacciyar sanarwa,” in ji ta.
“Sanarwar karshe da muka samu daga sakatare ta ce ba a yarda mu dawo bakin aiki ba, domin al’amari ne da ya shafi majalisar dattawa kai tsaye. Amma ga mu nan yau, kuma ina shirin yin dan lokaci a ofishina.”
Dawowarta ta haddasa dan rikici a kofar majalisar dattawa yayin da magoya bayanta suka dage sai sun shiga tare da ita.
Amma sai ta roki magoya bayan nata da su kwantar da hankali. “Wadanda suke son shiga, wannan ofishinku ne, hakkinku ne ku kasance a nan, kamar yadda yake hakkinku ku kasance a majalisar jama’a. Amma ina rokonku ku kasance cikin natsuwa da kwanciyar hankali,” in ji ta.
“Muradunku sun isa kunne, ayyukanku sun isa ido. ’Yan Najeriya suna alfahari da ku, ni ma ina alfahari da ku, har ma kakanninmu suna alfahari da ku. Yanzu kuwa zan shiga kawai.”
Sanatar an dakatar da ita ne bisa zargin karya wasu dokokin majalisar dattawa.
Sai dai a ranar 4 ga Yuli, Kotun Tarayya a Abuja ta bayyana dakatarwar a matsayin “mai tsanani kuma sabawa kundin tsarin mulki”, tare da shawartar majalisar dattawa da ta sake duba batun dawowarta bakin aiki.
Duk da wannan hukunci, shugabancin majalisar ya dage cewa ba za ta iya dawowa ba sai dai idan majalisar ta sake daukar sabon matsaya ko kuma kotu ta bayar da doka kai tsaye.
Dawowarta a ranar Talata ita ce karon farko da ta shiga ofishinta tun lokacin da aka dakatar da ita.
