Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Ogun ta dakatar da Sanata mai wakiltar Ogun ta Gabas, Gbenga Daniel, tare da Hon. Kunle Folarin, ba tare da iyaka ba bisa zargin aikata ayyukan cin amanar jam’iyya.
Rahotanni ta ruwaito cewa wannan mataki ya samo asali ne daga rikicin siyasa da ke ƙara kamari tsakanin Daniel da Gwamna Dapo Abiodun kan neman tikitin Sanatan Ogun Gabas a zaben 2027.
A makon da ya gabata, Daniel da Abiodun sun yi cacar baki a kafafen watsa labarai kan yunƙurin rushe wani ginin mallakar Daniel da ake zargin ya saba ka’idojin gine-gine, kafin lamarin ya kai gaban kotu.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na jam’iyyar, Nuberu Olufemi, ya fitar da yammacin Litinin, APC ta tabbatar da dakatar da Daniel bisa zargin ayyukan cin amanar jam’iyya.
Sanarwar ta bayyana cewa Kwamitin Aiki na Jiha (SWC) na APC a Ogun, a wani zama da shugaban jam’iyyar na jiha, Chief Yemi Sanusi, ya jagoranta a ranar 19 ga Agusta tare da halartar mambobi 16, ya amince da dakatar da mutanen biyu.
Rahoton ya ce, kwamitocin ladabtarwa na Ward 4 da Ward 6 a ƙaramar hukumar Sagamu sun gudanar da bincike kan zarge-zargen cin amanar jam’iyya da kuma rashin ladabi da aka yi wa membobin biyu.
Sanarwar ta kara da cewa:
“An aika wa waɗannan mambobin wasiƙar gayyata domin halartar zaman kwamitocin ladabtarwa da damar kare kansu, amma sun gaza zuwa, ba su aiko da rubutaccen bayani ba, kuma sun ki gabatar da hujjoji a madadinsu.
“Bugu da ƙari, kwamitocin sun samu rahoton cewa waɗannan mambobin na amfani da matsayinsu a jam’iyya wajen tsoratar da wasu da kuma hana mambobi bayar da haɗin kai ga binciken da ake yi.
“Saboda haka, kwamitocin sun yanke hukuncin dakatar da su na ɗan lokaci har sai an kammala bincike, domin kare martabar tsarin ladabtarwa da kauce wa tsoma bakin waɗanda ake tuhuma.”
Kwamitin Jiha (SWC) ya tabbatar da dakatarwar, inda sanarwar ta ce hakan na nuna jajircewar jam’iyyar wajen kiyaye ladabi da kuma mutunta kundin tsarin mulkinta.
