Babban Bankin Najeriya, Central Bank of Nigeria (CBN), ya gargadi gwamnatocin jihohi da su guji yawan dogaro da bashin gajeren lokaci da kuma karɓar kuɗin wuce gona da iri (overdrafts), yana mai cewa hakan na iya kawo cikas ga sabon tsarin da ƙasar ke shirin amfani da shi wajen daƙile hauhawar farashi.
Mataimakin Gwamnan CBN mai kula da manufofin tattalin arziki, Muhammad Sani Abdullahi, ne ya bayyana hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka shirya tare da Nigeria Governors’ Forum (NGF).
Ya ce sabon tsarin daƙile hauhawar farashi na bukatar cikakken haɗin kai tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi wajen tsara kasafin kuɗi da kula da basussuka.
A cewarsa, “yawan dogaro da overdrafts, ƙarin kasafin kuɗi da kuma bashin da bai dore ba na iya raunana tasirin manufofin kuɗi tare da ƙara matsin hauhawar farashi.”
Abdullahi ya jaddada cewa wajibi ne a kauce wa abin da ake kira “fiscal dominance”, wato yanayin da matsin lambar bashi zai tilasta wa CBN biyan gibin kuɗin gwamnati.
Ya kuma buƙaci jihohi su tabbatar da cewa duk wani bashi da suke karɓa ya dace da ƙa’idojin dorewar bashi, su inganta hasashen samun kuɗaɗen shiga, sannan su daidaita jadawalin kasafin kuɗinsu da yanayin tattalin arziki.
CBN ta bayyana manyan nauyin da ke kan jihohi a ƙarƙashin sabon tsarin, waɗanda suka haɗa da kiyaye ladabtar kuɗi, karɓar bashi cikin hankali, ƙarfafa kula da bashi da kuɗaɗen gwamnati, da kuma bunƙasa kuɗaɗen shiga na cikin gida.
Daraktan sashen manufofin kuɗi na CBN, Victor Oboh, ya bayyana tsarin daƙile hauhawar farashi a matsayin “tsari mai anfani ga kowa”, yana mai cewa yana rage rashin tabbas tare da ƙara amincewa da manufofin gwamnati. Sai dai ya lura cewa kashe kuɗaɗe da tarin basussuka a matakin jihohi na da tasiri kai tsaye kan yawan kuɗin da ke zagayawa da kuma hauhawar farashi.
A nasa jawabin, wakilin Nigeria Governors’ Forum, Farfesa Olalekan Yunusa, ya yaba wa CBN bisa haɗa gwamnatocin jihohi tun da wuri a wannan shiri, yana mai cewa dorewar zaman lafiyar tattalin arziki “ba za ta samu ba sai da haɗin kai mai tsari tsakanin dukkan matakan gwamnati.”
Taron ya samu halartar jami’ai daga fiye da jihohi 20, waɗanda suka bayyana goyon bayansu ga shirin gyaran tattalin arzikin. Wannan na zuwa ne yayin da bayanan Debt Management Office (DMO) suka nuna cewa bashin waje na jihohi ya ƙaru da dala miliyan 944 a shekarar 2025, lamarin da ke ƙara nuna muhimmancin karɓar bashi cikin kulawa.
