Ba Tirelan Dangote Ba ce Ta Haddasa Hatsarin Auchi – Inji Shaidu

Rahotanni na farko da suka yadu a kafafen sada zumunta sun ce trela mai ɗauke da siminti mallakar kamfanin Dangote ce ta haddasa mummunan hatsarin da ya auku a kan titin Auchi–Okpella–Okene, kusa da Omega Fire Ministry, a garin Auchi, karamar hukumar Etsako ta Yamma, Jihar Edo. Sai dai wani shaida ya karyata wannan ikirari.

Shaidan, mai suna Audu Omale, ya bayyana ainihin yadda hatsarin ya faru, inda ya ce:

“Wani trela na daban da ke ɗauke da siminti ya taho daga akasin hanyar trela na Dangote Cement (DCT) CNG, a kan wani gangaren hanya. Direban trelan ya kasa iya ja da baya saboda matsalar birki, ya afka kan wata mota, ya buge babur sannan daga ƙarshe ya daki gefen trela na DCT. Daga nan trelan Dangote ya kama da wuta.”

Omale ya ƙara da cewa, sakamakon hatsarin, mutane uku daga cikin motar da trelan na daban ya buge suka rasu, yayin da wasu biyu suka samu rauni daban-daban aka garzaya da su asibiti. Direban trela na Dangote ya tsere don guje wa afkawar jama’a.

A wani ɓangare na labarin, Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Edo (PPRO), CSP Moses Yamu, ya tabbatar da aukuwar hatsarin, yana mai cewa lamarin ya haɗa da manyan motoci guda biyu da kuma wata mota kirar GLK Mercedes Benz.

Yamu ya ce:

“Zan iya tabbatar muku cewa an samu hatsari a Auchi da rana tsaka, inda ya haɗa da manyan motoci biyu da kuma mota kirar GLK. An garzaya da mutane uku da ke cikin motar GLK zuwa asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsu. Daya daga cikin manyan motoci mallakar Dangote Cement ne, ɗaya kuma ba a gano shi ba. Trela na Dangote ya kama da wuta, daga baya aka kashe wutar.”