Tsohon sanata mai wakiltar Adamawa ta Arewa, Elisha Abbo, ya mika kansa ga Sashen Binciken Manyan Laifuka na ƴan sanda (FCID) a Abuja, bayan zargin yi wa wata ɗaliba ‘yar shekara 13 fyaɗe.
Iyayan ƙaramar yarinyar sun shaida wa manema labarai cewa tsohuwar ‘yar takarar gwamna a Jihar Adamawa, Sanata Aishatu Dahiru Ahmed, wadda aka fi sani da Binani, ta ziyarci gidansu domin roƙon su kada su tona asirin lamarin.
Sun kuma bayyana cewa bayan faruwar abin, Abbo ya rika tura kuɗi zuwa wurin mahaifin yarinyar, abin da suka ce yunƙuri ne na rufe batun.
A lokacin da aka wallafa wannan rahoto, Abbo na ci gaba da zama a hannun jami’an FCID.
Wannan ba shi ne karon farko da sanatan ya shiga rikici ba. A shekarar 2019, an kama shi bayan wani bidiyo ya bayyana yana dukan wata mata a wani shagon kayan wasa na jima’i a Abuja. Haka kuma, a baya-bayan nan wata matar aure ta zarge shi da yi mata barazana ta hanyar hoton bidiyon lalata.
Rahotanni sun nuna cewa fyaɗen da ake zargin ya faru ne a ranar 29 ga Yuni, 2025, a gidan Abbo da ke Katampe, Abuja.
Saharanews
